Yanda zaka hana a kira ka Da Private Number 2023

 

Yanda zaka hana a kira ka Da Private Number 2023



 Assalamu alaikum barkan mu da kasancewa a sabon darasin mu. Yan'uwa yau darasin mu yana da amfani kuma nasan kun dade kuna jiran wannan darasi da kuma application domin ganin kun magance duk wata matsala irin wannan.

 Application ne da zaka iya control din dukkanin kiran wayar ka domin kada a dame ka da kira.

 Da yawa zaka iya kasancewa da ana kiran ka da private number da kuma Unknown number sannan zaka iya saita adadin da kake so wata number ta kira ka.

Zan dan lissafo wasu daga cikin aikin application din nan.

1) Na farko zaka iya kunna duk wata kafa da idan an boye number a matsayin private number to kiran bazai shgo cikin wayar ka ba.

2) Na biyu zaka iya kulle duk wata number inde bakayi save dinta a wayar ka ba. Bazata shigo cikin wayar ka ba.

3) Na uku Zaka iya blocking din number baza a kira ka da ita ba

4) Na hudu zaka iya kashe duk wata number da ka zaba idan an kira ka da ita bazata shga ba. Amman baza'a gane kayi blocking din kiran ba.


Kamar yanda kuke gani a hoton sama. Dan misalan abinda app din yake yi.

 Akwai abubuwa da Dama wanda ya kamata kuyi amfani da wannan application saboda harda SMS wato message zaka iya blocking na wasu kamfanunuwa wanda baka yarda da su ba su daina turoma sakonni.

Zaka iya saita duk wata number da ta fara da wani number misali kamar duk number da ta fara da 070 ko 0703 ko farkon ta ko karshe to kiran bazai shigo wayar ka ba. Koda kuwa bakayi save din number a  wayar ka ba.


Kamar yanda kuke gani a hoton sama. Da duk wani adadin na rubutu da idan kana so kayi block din.


 Application ne gaba daya bashi da wahala wajen amfani da shi sannan zaka iya saita duk wani adadi da kake so bangaren kiran wayar da ake yima yau da gobe.


Kamar yanda kuke ganin hoton sama zaka iya amfani da schedule wajen idan ka saita lokachi da rana da number da kake so kada ta kira ka to idan lokachin yayi babu wanda zai kira ka  da number idan lokachin yayi.


Wannan application yana da matuqar amfanin da ya kamata ka dakko shi kayi amfani da shi a wayar ka.

Ga link din Application din a kasa zakaga na rubutu download da koren rubutu sai ka taba shine zaka sauke shi a wayar ka.

👇👇👇👇

Download

Previous Post Next Post