Yanda zaka kama Barawon wayar ka inda yake da hoton sa koda tafi shekara da BATA 2023

 Yanda zaka kama Barawon wayar ka inda yake da hoton sa koda tafi shekara da BATA 2023


Assalamu alaikum barkan mu da wannan lokachi yan'uwa na. Ina fatan kowa yana nan lafiya.

A gurguje kamar yanda kuka ga tallan videon da kuma title din videon to haka abin yake da gaske.

Sai de ka tsaya ka nutsu wajen karantawa da kuma fahimtar abinda nake nufi da kuma mallakar dukkanin Application din guda biyu.

Hanya ce da zaka iya gano wayar ka bayan ta bata ko kuma ta dan'uwan ka ko abokin ka batare da kunje police station ba.

Ta amfani da gmail din ka.

Application guda biyu ne da zaka gano wayar ka bayan ta bata.

Zanyi muku bayanin kowane applocation tare da muhimmanchin sa daya bayan daya.

     Application na farko: Shine zai baka damar gane hoton barawon wanda ya daukar ma wayar ko yayi kokarin budema securityn wayar taka. Da zarar ka saka applocation din a wayar ka tun yanxu to zaka saka gmail din ka shine app din zayyi aiki a wayar ka. Sannan application din gaba daya bashi da wahala wajen saitawa da kuma amfani dashi. 



 Duk wanda ya taba ma waya zai dauki hoton sa sannan ya tura ma ta asalin gmail din ka. Wanda idan ka bude gmail dinka zakaga dukkanin hotunan da aka turo ma wanda app din ya tyro. Sannan kowane hoto zaizo da location yanda zaka iya gane inda aka dauki hoton. Sannan ba lalle sai hoton yayi kyu ba koda an dauki hotoon zaka iya amfani da location wajen gano wayar taka.



 To shine kana taba location din shine application na biyu zai bude kamar yanda shima zanyi muku mabayjin sa a kasa.



Sannan shi wannan Application din zaka iya siyan Premium wanda aikin sa zai ninku kamar idan an sace wayar taka sannan an chanja Simcard acikin wayar to applocation din zai sanar da kai. Da dai sauran security wanda zai baka damar gano wayar ka dakanka batare dan kaje inda ake tracking ba.



     Application na biyu: Application na biyu shine zai baka damar gano inda wayar take. Idan ka taba link din da wancan Application din ya turoma shine zakaga asalin inda yake. Sannan zaka iya wipe din wayar wato ka goge komai zaka iya saka wayar tayi qara.

 


 Zaka iya kunna sauti koda wayar babu chaji zatayi qara kaji a inda take.


 Idan kana tunanin kamar akwai abu mai muhimmanchi acikin wayar taka gudun kada a ga sirrin naka zaka iya goge dukkanin abinda yake acikin wayar ta amfani da wannan application din.

Koda wayar babu security zaka iya saka security wanda babu yanda zaka iya amfani da wayar taka.

Zaka iya bi ta cikin wannan App din ka gano duk inda wayar taka take. 
To wannan hanyar ce kadai zaka iya gani dukkanin inda wayar ka take bayan ta bata ko an sace ta.
Ga link din dukkanin App din a kasa.

Application na farko zakaga download 1 shine idan ka taba zaka sauke shi acikin wayar ka.

Application na biyu zakaga Downlaod 2 sai ka taba ka sauke shi acikin wayar ka.
Previous Post Next Post