Yanda zakaga sirrin gidan ka batare da an sani ba ( Sabon sirri) 2023

 Yanda zakaga sirrin gidan ka batare da an sani ba ( Sabon sirri) 2023


Assalamu alaikum barkan mu da warhaka yan'uwa ya karin hakurin mu na yan'uwa wanda suka rasu. Allah yayi musu rahma yajikan su yayi musu afwa idan tamu tazo yasa mu cika da imani ameen.


 Yan'uwana a muslunchi yau darasin namu akan wani application ne mai tsadar gaske wanda ya kamata ka tsaya kaji ya app di  yake sannan dame-dame ya kunsa bayan nan sai ka dakko app din a wayar ka domin amfani da shi.


Application ne da zai baka damar gano dukkanin sirrin gidan ka ko shago ko office din ka ta cikin wayar ka.

 Na tabbata ka taba ganin cctv wanda zakaga a gidajen yan gayu suna amfani da su ko a shagon yan gayu hakan yake sakawa sai muga kamar mu bazamu iya amfani da shi a wajen sana'ar mu ba ko bazamu iya sakawa a gidajen mu ba.



  Shi yasa na kawo mana wata sabuwar fasaha wadda zata bamu damar amfani da wayoyin hannun mu a matsayin wannan cctv.

 Zakaga dukkanin abinda kake so ka gani batare da ka mallaki asalin cctv wadda yan' gayu suke amfani da ita ba.

 Da zarar ka mallaki wannan application din zaka saka shi acikin wayar ka. Sannan idan kana da wata wayar daban koda a ce tsohuwa ce to dasu zakayi amfani.

 Zaka ajje wannan tsohuwar wayar taka a inda kake tunanin baza'a ganta ba sannan sai ka dinga control din gidan naka ta ciki wayar hannun ka.

Koda kuwa baka garin ko kasar gaba daya.




 Zakaga dukkanin abinda yake faruwa a gidan ka ko shagon ka ko office dinka.

 Bugu da qari akwai abubuwan da zaka iya amfani dashi wajen jin sauti ko record.

  Abubuwan da app din ya kunsa

 Ya kunshi abubuwa da dama wanda zakayi amfani dashi kaji dukkanin abinda kake buqata gasu nan a kasa kamar haka.

 1) Zakayi amfani da application din wajen ganin dukkanin abinda yake faruwa a lokachin da kake kalla wato Live

2) zaka iya danna record yana ajje ma dukkanin abinda wannan application din ya dauka na video koda idan ka dawo ka dauki wayar zaka iya kunnawa ka kalla.

3) zaka iya kunna sauti kana jin dukkanin abinda ake fada a lokachi domin zai daukar ma videon tare da sauti mai kyu.

4) Zaka iya amfani da camera gaba ko ta baya ta amfani da wayar ka koda baka kusa ko gari daya da gidan naka ko office.

5) Zaka iya hada wayoyi sama da guda biyu domin amfani da su kuma kayi comtrol din su ta cikin wayar ka.




         Abinda zakayi

 1) Idan ka dakko app din duka zaka saka su a cikin wayoyin naka guda biyu zai baka damar saita wadda idan zaka ajje ta da kuma wadda zakayi amfani da ita wajen control sannan babu wahala wajen saitawa.

 2) Zaka sami inda baza'aga wayar da zaka ajje a wajen ba kamar de yanda kuke ganin inda ake ajje asalin cctv zakuga a sama ake ajjewa. To itama sai ka sami sama sannan inda baza'a ganta ba. Bayan nan tayi saiti sosai da inda kake so ka gani.

Ga link din Application din a kasa zakaga an rubutu download da koren rubutu sai ka taba ka dakko shi a wayar ka.

Download

Previous Post Next Post