Application mai abin mamaki. Zaka saurari waka (music ) biyu a kunne daya 2023

 

Application mai abin mamaki. Zaka saurari waka (music ) biyu a kunne daya 2023

Assalamu alaikum barkan mu da sake kasancewa a yau a sabon darasin namu. Yau darasin mu akan wani application mai abin mamaki wanda zai baka damar sauraron waka guda biyu a kunne daya wato ( headphone ). Wato abin nima ya bani mamaki matuqa musamman da nayi amfani da shi. Na tabbata kaima ka qagu domin kaji ya bayanin wannan Application yake.



Insha Allah ku biyo ni har karshen rubutun zanyi muku cikakken bayanin yanda application din yake.

         KARIN BAYANI


 Application din amfanin sa shine zaka kunna waka konkaratu guda biyu a lokachi daya kuma a saurara a kowane kunne da yake a jikin headphone. Kai koda karatu da waka ne to kowane kunne zaiyi abinda ka kunna ne.

Wani lokachin abokin ka ko budurwar ka zata takura ma a kan cewa sai ka kunna mata wani karatu ko waka wand akai kuma a lokachin bashi kake so ka saurara ba. To da taimakon wannan Application zaka iya kunna abubuwan guda biyu. Da abinda kake so ka saurara da kuma abinda budurwar taka take so ta saurara a lokachi daya.

Kuma batare da sautin ya hade ba. Kowane zaiyi nasa sautin sannan normal kamar yanda ka saba kunna abu ta cikin wayar ka ka saurara a headphone.


Sannan wajen amfani da application din babu wahala saboda kana bude shi zakaga ya nuna ma left side da kuma right side. Wato idan ka taba wajen daya daga cikin zai baka damar dakko wakar da kake so ka kunna. A lokachin idan ka kunna ta to iya abinda ka zaba ne zaiyi. Misali.: Left side yana nufin hannun hagu kenan sannan right side  yana nufin Hannun Dama. To duk lokachin da ka zabi left wato hagu to headphone ma bangaren kunnen hannun hagu shine zayyi wannan wakar da ka zaba. Haka shine bangaren Damar.





To kaga zaku iya amfani dashi ku biyu a lokachi daya kamar yanda kuka ga misalan sa a hoton sama zakuga mace da namiji ne suke sauraron sauti daban daban a headphone guda daya.

 Wato sai ka dakko applocation din ka kunna sannan zai baka mamakin da baka taba tunani ba.

Ga link din Application din a kasa zakaga nace download da koren rubutu sai ka taba ka sauke shi a wayar ka sannan kayi amfani da shi. 

Bugu da qari application din ya sami yabo sosai ga wadanda suka dakko shi a playstore.


👇👇👇👇👇

Download

Previous Post Next Post