DATAR LAYIN KA TANA KAREWA DA WURI?. GA MAFITA

        DATAR LAYIN KA TANA KAREWA DA WURI?. GA MAFITA

Assalamu alaikum barkan ku da warhaka yan'uwa yau darasin mu akan hanyar da zaka hana wayar ka shanye ma datar waya ko layin ka.

Da yawa muna fama da wannan matsala na ganin da zarar mun saka data a wayar mu lokachi kadan ta qare.

 To abinda baku sani ba shine a dukkanin applications da suke acikin wayar mu sukan iya shanye mana datar wayar mu koda kuwa baka shiga cikin su ba.

 Sannan Application din yazo acikjn wayar ka ne konkuma kaine ka saka shi da hannun ka domin amfani dashi.

 Sukan iya amfani a background na wayar ka. Sannan akwai application din ma da ba'a ganin su amman sukan dauki bayanan ka ko su dauki datar layin ka.

 Sannan wannan hanya zata baka damar kashe dukkanin abinda baka so a ganka mislai kamar whatsapp zaka iya kashe datar sannan ka kuma hau tiktok ko facebook amman da yake ka kash datar whatsapp baza'a ganka a lokachin ba.

 Shi yasa na kawo mana wani application da zai baka damar kashe duk wata kafa da datar wayar ka take qarewa da wuri.

 Da farko de shi wannan application bashi da wahala wajen budewa da kuma amfani da shi.

 Sannan bashi da nauyi wajen dakko wa.

Sannan baya daukar bayanan da bakasan da shi ba.

 sannan ya sami mutane sama da million daya sun dakko shi a playstore.

 Da zarar ka dakko applocation din sai ka bude shi shine zaka ga ya jero ma dukkanin application ma wayar ka wanda ka dora da hannun ka da kuma wanda yazo acikin wayar.


kamar yanda kuke ganin misalin shi a hoton sama da na ajje muku.

 bayan nan dukkanin application din a gefen sa zaka ga wata alamar duniya.

 To yanzu idan kana so ka kashe datar wani application din sai knnemo shi bayan kazo daidai application din to wajen alamar duniyar nan sai ka taba.  Kana tabawa zakaga wannan alamar duniyar ka cancel. To dukkanin wani application da kake so kankashe domin kada ya sha ma datar wayar ka sai kabi daya bayan daya ka danna. Bayan ka gama zabar wanda kake so ka kashe.

A kasan zaka wata makunna inda aka rubuta Off and On. To a lokachin da ka bude app din zakaganshi a Off yake to sai ka danna ON din. Bayan ka danna On din shine zai kashe ma dukkanin application din da ka zaba wajen ganin ka hana shi sha maka datar wayar ka.

 Inde ka danna wannan ON din to koda ka kunna datar wayar ka wadannan application da ka zaba baza su sha maka datar wayar ka ba.

 Koda kuwa whatsapp ne idan ka shiga zakaga babu network abinda zai fada ma. Sai de idan kashiga application din sai ka cire wannan cancel din da ka danna akan whatsapp din.

 Wannan itace hanyar da ake amfani da wannan application din.

 Ga link din application din nan a kasa zakaga an rubuta download da koren rubutu. Sai ka taba shine zai sauke ma a wayar ka.


Download

Previous Post Next Post