Sirrin da yake cikin code din xender😄😄

 

( SIRRI ) Kaga abinda ke cikin Code din XENDER



Assalamu alaikum warahmatullahi wa barakatuh. Barkan mu da warhaka. Yan'uwa yau darasin mu akan wasu application guda biyu wanda zasu baku damar boye sirrin ku.

 Da farko zan fara magana akan qrcode na jikin xender wanda muke scanning kafin mu hada waya guda biyu wajen tura waka ko hoto ko video ko kuma wani file haka. 

 Ina magana ne akan irin wanna code din wanda na ajje muku hoton sa  a kasa.

 



 To da yawa nasan mutane suna manakin menene acikin wannan code na xender. 

 Da farko de shi wannan code din ana kiran shi da QRCODE. Wanda mafi yawan chi zakaga akwai application da website ko kuma idan kaje mall wato shopping zakaga a jikin kaya akan saka su.

 To shi wannan QRcode wani sirri ne da ake buyo wani rubutu ko hoto ko wani link ta ciki wanda babu wanda zai gane wannan rubutun ko link din sai idan ka san shi ko ka san Application din da zai fassara ma wannan abinda aka boye aciki.

Shi yasa na kawo mana su duka application din guda biyu wanda zasu baka damar boye sirrin maganar ka ko hoton ko ko wani bayani domin gujewa masu bibiyar chat din ka.

 APPLICATION GUDA BIYU:


Application ne guda biyu wanda zaka iya amfani dasu wajen kirkirar qrcode sannan dayan Application din zai baka damar fassara wannan qrcode din da ka gani.

 (1) Application na farko shine zai baka damar rubuta dukkanin abinda kake buqata koda message ne ko kuma hoton ka. Bugu da qara koda link din website ko na application ko kuma kowane kalar link tare da logon kaya ko hoton ka a hade.


Kamar yanda kuke ganin misalin sa a hoton sama.

 Zaka iya dora koda link din profile din ka na dukkanin social media. Sannan ka turawa duk wanda kake so ka turawa koda ta whatsapp ko ta wani chat ko kuma kayi print dinsa a jikin paper ko invoice ko riga ko kuma Littafi.

 



 Zaka iya design din sa yanda kake so wajen hadawa yayi kyu sosai sannan kayi amfani da shi.

Ga link din application din a kasa zakaga an rubuta download 1 da koren rubutu domin amfani da shi.

👇👇👇👇👇👇👇

Download 1


 (2) Application na biyu shine zai fassara ma dukkanin abinda aka rubuta a jikin Qrcode koda kowa Code din jikin Xender ne wanda muke yawan gani.

 Sannan koda wani shopping kaje kaga ni a jikin wani kaya zaka iya scan din shi. Shi wannan application din zai fada ma dukkanin abinda yake a kunshe a ciki.

 Bugu da qari koda a wajen WIFI kaga an ajje wannan Code din zaka iya scan ning domin ganin wannan password na wifi din.



Sannan ba yawa QRCODE yake fassarawa ba zaka iya fassa Barcode wanda muke gani a jikin kwalin wani abu haka.

Ko a jikin babban kaya.



 Irin wannan misalin kenan wanda na ajje muku a hoton da yake sama.

Sannan koda a jikin invoice ko receipt k ganshi zaka iya scan nin din sa ta cikin wannan Application din.


Ga link din Application din shina a kasa zakaga an rubuta download 2 da koren rubutu sai ka taba ka sauke shi acikin wayar ka.

👇👇👇👇👇👇

Download 2


Previous Post Next Post