Tabbas ana bibiyar chat din ka a whatsapp baka sani ba😢 2023

 

Tabbas ana bibiyar chat din ka a whatsapp baka sani ba😢

Assalamu alaikum barkanmu da warhaka abokanai na. Ina fatan kowa yana cikin farin ciki da aminchi Allah yasa Hakan ameen.

 Allah ya bamu abinda muke nema na alkhairi ya bamu ikon godiya gare shi mahaliccin mu ameen.

Yan'uwa kamar kullum yau ma wani application mai amfani da na kawo mana.

 Domin kare sirrin dukkanon sakonnin da kake turawa domin kada wani ya dinga bibiyar chat din ka.

 A whatsapp ko a normal message ko dukkanin sakonnin da muke turawa.

 Domin Application ne da zai bamu damar boye wani rubutu zuwa wani code ma computer wanda ya kamata ku san shi.

 Da farko de nasan tunda nace muku code din computer akwai wanda sun fuskanchi abinda nake nufi domin yaren computer babu wanda yake gane shi sai ita kadai.

 Da farko de idan ka mallaki application din bayan ya bude ma idan kaine zakayi rubutun zakaga Encrypt to nan zaka taba.



Bayan ka taba zai baka damar zabar yaren da kake so kayi amfani da shi wajen chanja chat din naka.

Bayan ka zabi yaren na da kake so kayi amfani da shi.
Zakaga girin da zakayi rubutun idan kuma already kayi rubutun kana son chanja shi ne. Sai ka copy din sa sannan kayi paste din nasa.
To zakaga a kasa ya baka zuwa yaren da ka zaba.
Kamar yanda kuke gani a misalin kasa.
👇👇👇👇👇


  To sai kayi copy na abinda ya chanja ma sai kaje ka turawa wanda kake so ko wanda kuke yin chat din dashi.

 Dole sai kayi copy din sa. To normal ko a whatsapp din ma zakaga wannan rubutun da ka copy anan shi zaka gani. Sannan shima shi zai gani.

 Kawaia abinda zakayi idan zai fassara rubutun shine ya yi copy din abinda ka tura masa.

 Bayan nan sai ya bude irin application din ko nace wannan application din domin shima dole sai ya mallake shi sannan.

 Bayan nan sai ya taba Decrypt sannan sai ka fada masa da irin yaren da kayi rubutun.


Bayan ya taba Decrypt din zai bude masa wajen yarikan kamar yanda yayi maka a farko kenan.

 To sai ka fada da yaren da kayi masa wannan sakon.


 Yana budewa sai yayi paste din wannan rubutun da ka tura masa ta whatsapp din to shi application din fada masa abinda ka rubuta.

 Kaga gaba daya koda mutum yana bibiyar ku bazai gane abinda kuke magana akai ba.

 Sannan koda yasan da application din da kuke amfani amman bazai san yaren da kuke maganar da shi ba.

 Wato app din yana da amfani ka dauke shi da muhimmanchi sosai domin ko ba yau ba zaka son yin amfani da shi.

 Ga link dinsa nan a kasa ka taba sai ka sauke shi a wayar ka.

Zakaga na rubuta download da koren rubutu.

Download

Previous Post Next Post