Yanda zaka ajje sirrin ka (password,hoto,video) koda ka chanja waya bazasu goge ba

 Yanda zaka ajje sirrin ka (password,hoto,video) koda ka chanja waya bazasu goge ba


Assalamu alaikum barkan mu da kasancewa a wani sabon darasin.

Yan'uwa yau wani application na kawo mana wanda zai baka damar ajje dukkanin abinda kasan sirrin kane sannan koda ka chanja waya wannan sirrin bazai bata ba.

 Kamar yanda muka san Turawa suna samun Diary wajen rubuta abubuwan da ya shafi rayuwar su na sirri haka zalika muma mukan sami dan wani littafi ko paper wajen rubuta password ko wani labari ko wata wasika domin ajjewa saboda wata rana.




 To yan'uwa yanzu an waye a waya ma zaka iya rubuta dukkanin abubuwan d akake buqata sannan da tsari masu kyu koda kuwa ma ka chanja waya batare da shan wahala ba kana dakko irin application din kawai kana saka gmail din ka zakaga wadannan rubutun da kayi sun dawo zuwa wayar da ka chanja.

 Dukkanin wani password da muke tunanin yana da amfani ko wani rubutu to ya kamata muna adana sa a cikin ire-iren wannan application smman wanda mukasan suna da sirri sosai.


Kana dakko application din bayan ka saka gmail naka zakaga inda aka rubuta Backup bayan ka taba to koda ka chanja wayar zakaga wajen Restore idan ka danna restore din shine duk abinda ke cikin tsohuwar wayar ka zasu dawo kan sabuwar wayar.

Ga link din Application din a kasa sai ka taba shine zaka sauke app din a wayar ka domin amfani da shi.


Download

Previous Post Next Post