Yanda zaka tura kowane application kyuta.

  


Yanda zaka tura kowane application kyuta.



Assalamu alaikum barkan mu da wannan lokachin. Yan'uwa yau darasin mu akan wani application ne da zai baka damar tura kowane kalar application ta cikin wayar ka zuwa wata wayar daban batare da Xender ko USB ko wifi ballantana Data.

 Wato akwai application da yawa wanda bama lura da irin aikin su har sai idan wani lokachin buqatar abin ya zo maka.

 Wani lokachin zakaga kana so ka turawa wani abokin ka application ko kuma zaka turo zuwa wayar ka to zaka rasa yanda zaka tura wannan application din zuwa wayar ka.

 Sannan wani lokachin zakaga babu xender a wayar taka ko a wayar abokin naka.




 Ta wannan application din zaka iya turawa.

 Sannan koda ma kana da xender ko bluetooth kana son tura wani application din amman xender da yawa bata ganin system application.

 System application: Duk da nasha yi muku bayani akan sa. Shine wanda waya take zuwa da shi. wani ma gaba daya baza ka ganshi acikin wayar ba ballantana ka tura irin su . Google service da sauran su.

To ta amfani da wannan application zaka iya turawa wayar ka kowane kalar application sannan kayi amfani da shi.



 Wannan application din ya sami mutanen da suka dakko shi a playstore sama da mutum millions 10M+.

 Ga link din Application din a kasa zakaga an rubuta download da koren rubutu sai ka taba ka sauke shi a wayar ka.






Download

Previous Post Next Post