Application na sirri Yanda zaka ajje duk wani app na wayar ka inde bazai bata ba har abada

Application na sirri Yanda zaka ajje duk wani app na wayar ka inde bazai bata ba har abada

Assalamu alaikum barkan mu da warhaka yan'uwa na  a muslunchi. Yau darasin mu akan wani boyayyen ilmi ne wanda ba kowa yake kawo hankali akan sa ba.



 Domin da yawa akwai ire-iren wadannan abubuwa amman koda wasa babu wanda zai fahimchi asalin abin.

Misali. Dukkanin wani application da muka dora kan wayar mu muke amfani da shi inde a playstore muka dakko shi to fa iya kan waya yake hawa baya zama akan asalin Storage na wayar ko kuma kan memory na wayar.

Inde kaga application ya hau kan memory na waya to ka tabbatar da cewa ta Xender aka tura ma ko ta bluetooth ko wani abu makamanchin wannan. Amman inde a playstore ka dakko shi to sai de kawai kayi amfani da shi a wayar ka sannan duk lokachin da ka yi uninstall din sa to pa sai de ka qara zuwa playstore ka dakko shi. Amman babu wata folder ta cikin wayar ka da take ajje ma irin wadannan application.

 To shi wannan  Application da na kawo mana zai baka damar ajje dukkanin wani application wanda ka dakko a playstore zuwa kan memory na wayar ka. Batare da wata shan wahala ba kawai kana bude application din zai nuno ma dukkananin wasu application da ka ke amfani dasu akan wayar ka. To sai ka zabi wanda kake so ya zauna akan wayar taka kawai kana danna kan sa to zai sauka automatic akan memory na wayar taka.

 Da zarar ka shiga ciki file manager na wayar ka zaka nemo folder da ya ajje ma to zaka ganshi aciki.

 Sannan kowane kalar application ne. 

Irn user application ko System application. Dukka shi wannan application din zai ware ma su daban daban saboda gudun samun matsala.


Kamar yanda kuke gani cikin misalin wannan hoton saman idan kukayi la'akari akwai installed app da kuma system app.

Installed App shine ( User app). Shine wanda ka dora mata misali whatsapp tiktok ko wata game haka. System app shine wanda wayar take zuwa dashi. idan ka cire daya daga ciki to wayar ka zata dinga baka matsala.

 Ga kink din Application din a kasa sai ka tana ka sauke shi a wayar ka.

👇👇👇👇👇👇



Download

Previous Post Next Post