Yanda zaka bude whatsapp da number america ko france 2024

 

Yanda zaka bude whatsapp da number america ko france 2024



Assalamu alaikum barkan mu da wannan lokachi. Yan'uwa yau darasin mu akan wani application ne mai muhimmanchin da zai baka damar mallakar number waya ta kowace kasa kake buqata sannan kayi amfani da ita bangaren bude whatsapp ko telegram ko amsas dukkanin wani abu da ya danganchi otp idan zaka bude wani account ma application ko ma wani website.



  Da zarar ka shiga application din zai nune ma service da kuma activation wanda shi service din shine zai baka damar zabar abinda kake so kayi da number misali idan bude whatsapp zakayi da ita ko telegram ko kuma kana so kayi forward na kiran wayar ka zuwa virtual number to zaka zaba da kanka. Bayan ka zabi abinda kake so kayi da number wayar shine zai baka damar kuma ka zabi da wace kasa kake so ka mallaki number wayar kasar. Amman da adadin credit din da ake buqata wanda za'a baka wannan number wayar. Akwai bangaren activation shine idan ka zabi number wayar dukkanin abinda kayi da number wayar ka message ne ko na otp na wani code to zaka ganshi a nan gurin.


Amman maganar gaskiya ba free bane kamar yanda da yawan mu burin mu kenan komai sai de mu mallaka free koda dan kudin ka baza ka saka ka mallaki abu ba.

 Hanyar da zaka mallaki number wayar ta cikin wannan Application din shine bayan ka zabi services da kuma kasar da kake so ka sami number shine zakaga adadin coins da ake buqata kafin ka mallake ta.

  To idan baka da coins din ko credit din achan sama zakaga alamar gurin coins bangaren hannun daman ka kenan. Idan ka taba zakaga adadin coins da kuma kudin wannan coins din. Wanda iya wanda kake so ka mallaka na credit din shine zaka zaba sai kabi hanyar da zaka siya.

 Bayan ka siya shine sai kaje ka mallaki wannan number wayar.


Bugu da qari zaka iya zabar kowane kalar yare kake so kayi amfani da shi acikin application din.


 Ga link din application din a kasa za kaga na rubutu download d akoren rubutu sai ka taba ka sauke shi a wayar ka.

👇👇👇👇

Download

Previous Post Next Post