Yanda zaka gano duk samfur na Shuka ta cikin wayar ka 2024

 Yanda zaka gano duk samfur na Shuka ta cikin wayar ka 2024


Assalamu alaikum barkan mu da warhaka yan'uwa yau darasin mu akan wani application mai amfanin da zai baka damar gano dukkanin rayuwar tsirrai ko bishiya ta amfani da wayar ka.

 Da zarar ka mallaki wannan application din kawai duk wata bishiya da kake so ka gano sunan ta da kuma yanda take rayuwa da dukkanin wasu abubuwan da zasu taimaka mata domin girma ko maganin abinda take a guri duk wannan application din zai fada ma.

 Application ne da ba kowa zai san muhimmanchin sa ba saboda ba kasafai muke lura da cututtukan da shuka ko bishiya suke yadawa ba. Illa iyaka kawai munga shuka ta burge mu sai muje mu dakko mu dasa a inda muke so mu shuka ta.

 Amman muddun mukayi wata shukar a wani gurin ya kan bawa gurin wata cutar ko ya saka ginin ba ko gidan ka.



 Ko gaba daya kaga wata bishiyar amman bakasan sunan ta ba. To idan kana da wannan application din kawai zakayi scanning din wannan bishiyar ko shukar to application din zai fada ma sunan ta da dukkanin  yanda take rayuwa.

 Sannan zai taimakawa dukkanin wanda yake karanta forestry a makarantum gaba da scondry.

 



Zaka iya rubuta sunan  shuka ko bishiya ko ka dauki hoton ta ta camerar wayar ka ko kuma idan kana da hoton kawai sakawa zakayi a application din zai fadama komai akan shukar ko bishiyar.



 Ga link din application din a kasa zakaga an rubuta download da koren rubutu idan ka danna shine zai baka damar ka sauke application din a wayar ka.

👇👇👇👇👇👇👇👇


Download

Previous Post Next Post