Yanda zakayi control din wayar ka batare da ka taba ta ba 2024

 Yanda zakayi control din wayar ka batare da ka taba ta ba 2024 ( Call Announcer )

Assalamu alaikum barkan mu da sake kasancewa a wani sabon darasin. Yan'uwa yau darasin mu akan wani application ne wanda zai taimaka ma wajen ganin ka saukaka amfani da wayar ka koda baka kusa da ita. Domin application ne da zai dinga fada ma sunan wanda ya kira ka sannan ya fada ma daga garin ko gurin ( location ) din da ya kira ka. Haka zalika SMS wato ( message ) zai fada ma wanda ya turo ma da wannan sakon da kuma abinda sakon ya kunsa koda baka gaba wayar ka. Sannan wannan sakon wato SMS din na normal message ne ko na whatsapp wanda aka turo ma ko dukkanin wani notification da aka turo.

 Amfanin wannan application din ko baka kusa da wayar ka sannan koda kana aiki to idan akayi ma daya daga cikin wannan abubuwan da na lissafa ita wayar da kanta zata fada ma komai.


 Bugu da qari zaka iya saita wannan notification din ko kiran wayar da hasken flash light din ka.

  Da zarar an turo da wannan sakon to hasken wayar taka zatayi haske sosai har sai ka gane wayar taka akwai abinda take nufi. Sannan kiran wayar ma abinda zatayi ma kenan.

 Sannan koda baka so saboda yawan kiran da akeyi ma a wayar baka so duk kira ta dinga fada ko tayi ma hasken zaka iya zabar wani adadi ma contact din ka ko ka ware mutum daya wanda kiran shi yana da muhimmanchin da idan ya kira kankoda baka kusa da wayar taka ita wayar ta fada ma ya kira ka ko ya turoma da sakon.


 Zaka iya saita duk yanda kake so application din ya kasance domin gudun kada ya takurama ma.

 Bangaren kiran wayar ne ko bangaren turo sakon ne da kuma bangaren hasken fitilar wayar taka.

 Zaka iya saita yanda hasken zai kasance ko yanda ringtone din wayar taka zai kasance.





 Sannan da duk wani abu da ya danganchi bayanan wanda ya kira ka idan baka da number sa.

  Sannan shi wannan application ba iya wanda suke gani zayyiwa amfani ba. Zai yiwa wanda Allah ya jarabta da rashin gani idan aka saita musu shi a wayar su zasu dinga gane wanda ya kira su ko ya turo musu da sakon wayar ko whatsapp batare da suna tambayar na kusa da su ba.

 Ga link din Application din a kasa zakaga an rubuta download da koren rubutu sai ka taba ka sauke application din a wayar ka.

👇👇👇👇👇👇👇😀

Download

Previous Post Next Post