Avee player Abin burgewa ga masu amfani da waya

 Avee player Abin burgewa ga masu amfani da waya 





Assalamu alaikum barkan mu da wannan lokachi. Yan'uwa ya sanyi ya kuma qara hakuri damu. 

Yau darasin mu abin burgewa ne wanda nasan da yawa mundade muna jiran wannan darasi domin wani application ne da yawa mutane zasu son sanin koda ace sunan sa ne ballantana link din sa da kuma yanda ake amfani dashi.

 Wannan application din shine wanda zai baka damar kirkirar spectrum na wakoki ko na karatun qur'ani ko kowane kalar sauti na music Sannan kayi editin din dukkanin abinda kake so ka chanja acikin application din zuwa naka na wakar ko karatun. Misali zaka iya dora hoton ka ko hoton mai wakar ko kuma wani abin burgewa domin dukkanin wanda ya mallaki wannan wakar ko ya mallaki wannan karatun zai buegeshi sosai.

 Sannan zaka iya dorawa a tiktok ko a youtube domin zai zamo kamar video kenan.



 Kamar yanda na nuna muku misalin wannan application din  acikin videon da dukkanin abubuwan da ake iya hadawa dashi.

To gaba daya amfani da application din bashi da wani wahala domin daga bude application din ma shi application din zai dinga fadama dukkanin abubuwan da kake so sannan da abinda zakayi har ya kasance ka kirkiri mai kyu da kuma yanda zakayi save dinsa a wayar ka.



Kamar yanda kuke gani a hoton sama zaku ganshi ta inda ake saita hotuna da kuma kalolin da kake so background ya kasmace abinda yasa na dan dakko muku iya nan saboda nasan mutane zasuga abin yayi musu yawa sosai to idan kuka nutsu zakuga gaba daya abin gida biyu ne sannan kawai duk inda kukaga Image shi zaku taba sai ku dakko hoton da kuke so ku dora acikin wannan wakar ta cikin wayar ka.

 Link din application din yana kasa zakaga na rubuta download da koren rubutu a kasa sai ka taba ka sauke shi a wayar ka.

👇👇👇👇👇👇

Download

Previous Post Next Post