Yanda ake hada Cartoon a waya abin sha'awa 2023

Yanda ake hada Cartoon a waya abin sha'awa 2023



Assalamu alaikum barkan mu da warhaka. Yan'uwa yau darasin mu akan application din da mutane da yawa suke buqatar su san dashi wanda zakaga ana hada cartoon din abin burgewa musamman ma hotunan kasar hausa ko na wani dan siyasa musamman irin kwankwasiyya ko wani abin burgewar. Na kasar hausa ko ya zana ma dukkanin abubuwan da kuke so ka kirkira.

 Shi wannann application din zai hadama cartoon din dukkanin abinda ka ke so inde ka rubuta masa ko da labari ne.

 Yanzu misali idan kana so ka kirkira hoton wani mutumin ko hoton wata kasuwa ko gari. To zakayi cikakken bayanin dukkanin abinda kake so ya fito acikin hoton lokachin da application din yake zana ma.


misali kamar hoton da yake a sama zaku ga mutum ne namiji da kuma mata hudu sannan da yara biyu ga wasu a zaune wasu kuma a tsaye sannan akwai tabiri ma abinchi akai. Sannan dukkanin su suna cikin nishadi.

 To kamar yanda na danyi wannan bayanin da hausa a sama akan hoton to irin haka zakayi a cikin application din shine zai futar ma da dukkanin abinda kake so ya kasance acikin hoton da zai fito ma.

 Koda hoton kane ko hoton wani dan siyasa ko wani abu to cikakken bayani zakayi akai shine zai fitoma da komai acikin hoton.

 Sannan wannan application din dukkanin wayoyin na android da kuma iphone kowane akwai application din su.

 Ga link din su nan a kasa zakaga an rubuta download da koren rubutu sai ka taba zaka sauke shi akan wayar ka. Amman link din android kawai na ajje. Masu iphone dai suje appstore su dakko nasu.

 Bayan ka bude application din zakaga App kamar yanda kuke gani acikin hoton kasa. Sai ka taba Apps din.


A kasan wadannan Menu din inda zakaga a farko akwai HOME na karshe daga hannun Dama kuma akwai Apps sai ka taba. Idan ka taba zakaga ya qara kawo ma wasu menu din sai ka nemo IMAGE sai ka taba bayan ka taba zai baka dama kirkirar Account. Suna da kuma password da gmail din ka.



 Bayan ka kirkiri account din zai nunoma hanyar da zakayi bayanin abinda kake so shi application din ya kirkirar ma.



 Bayan kayi rubutu zakaga Create AI bayan nan zakaga Creating sai ka dan Jira kadan zai qarasa ma bayan ya gama zai fitoma da dukkanin rubutun da kayi sannan zakaga hotunan da yawa sai ka zabi wanda yafi kyu.

 Sannan sai ka taba ka sauke shi akan wayar ka.

Wannan shine dan abinda ya kamata ka sani akan application din.

 Ga link din application din a kasa sai ka taba ka sauke shi akan wayar ka.

👇👇👇👇👇👇👇

 Download

Previous Post Next Post