Sabuwar Fasaha Yanda zaka mayar da katin hoto zuwa wayar ka 2024

Sabuwar Fasaha Yanda zaka mayar da katin hoto zuwa wayar ka 


Assalamu alaikum barkan mu da warha yan'uwa ina fatan kuna cikin koshin lafiya.

Yau darasin mu akan wani application ne da zai baka damar mayar da dukkanin wani decument hard copy zuwa soft copy na waya kenan.

 Menene banbanchin Hard copy da kuma Softcopy.

Hard copy shine normal takarda wadda kake rikewa a hannun ka ta hoto ce ko kuma wani handout ko wata takarda ta karatu duk de wata takarda da kake iya rikewa a hannun ka sannan ka karanta ta. Ita ake kira hard copy abinda zakaniya gani sannan ka taba shi a matsayin takarda kenan.

 Softcopy shine wanda yake acikin wayar ko computer zaka iya gani amman bazaka iya rike shi ba. Zaka iya ganin wata takarda ta sanarwa ko wani hoto amman bazaka iya rike shi ba to shine ake kira da softcopy.

  To shi wannan application din zai baka damar mayar da dukkanin wata takarda hardcopy zuwa cikin waya ko computer a matsayin softcopy.

 Dukkanin wata nau'ij takarda na hoto ko na makaranta ko na wata sanarwa dukkanin su zaka iya mayar da ita zuwa ta waya kamar yanda kuke karanta wannan rubutun normal. Sannan zaka iya amfani da shi wajen neman aiki ko wani karatu haka. Sannan zaka iya gyara dukkanin wani mistake ko ka mayar dashi zuwa wani project naka.


Kamar yanda kuke ganin hoton sama zakuga takarda ce a hannu sannan an dauki hoton ta ta cikin wannan Application din.


Sannan a hoton kasa kuma zaku ga ta koma normal Softcopy a cikin waya kenan.


Sannan koda ID card din ka ne zaka iya mayar dashi acikin wayar ka sannan ka dinga amfani dashi koda a wajen aiki ne ko a wani application ko wani platform normal zai koma softcopy.

 



Tare da hoto gaba daya kamar yanda kuke ganin misalan su a sama kenan.

 Ga link din application din nan a kasa sainka taba ka sauke shi akan wayar ka.


Download

Previous Post Next Post