Ka gaggauta mallakar wannan Application din na Qur'ani a kowace kalar waya 2024

Ka gaggauta mallakar wannan Application din na Qur'ani a kowace kalar waya 2024






Assalamu alaikum barkan mu da warhaka yan'auwa yau darasin mu akan abinda ya kusan zama dole sai mun mallaka a wayar mu domin tsira duniya da lahira saboda application ne na qur'ani.

 Dukkanin wasu hanyoyin da ya kamata ace kabi wajen koyon karatun al'qur'ani ko kuma karantawa ko dukkanin wasu abu da zai taimaka ma wannan application din ya hadema komai.

 Da zarar ka mallaki application din farko zai baka dukkanin malamin da yayi karatun qur'ani wato wanda yayi shura to akwai shi acikin wannan application din. Zaka iya zabar wanda kake so domin ya karanta ma dukkanin wata surah ko aya domin iya waya saboda zaka iya saitawa acikin malamin yana karanta ma sannan ayar ko surah tana fitowa a jikin screen din wayar ka sannan tare da fassarar kowace aya sannan fassarar zaka zabi yaren da kake so ka karanta fassarar.



 Sannan zaka iya saitwa kawai malamin zaka saurari karatun direct ta cikin application din.



 Akwai hanyar da zaka iya karantawa da kanka dukkanin inda kake so a cikin qur'ani sannan zai fito ma a matsayin shafi-shafi na qur'ani duk yanda kake so.

 Akwai hanyoyin da zaka bi wajen gyara haddar qur'ani ta cikin wannan application din.

 Bugu da qari dukkanin ranakun da suka zo application din zai dinga tunatar da kai wasu ayoyi da ya kamata ka karanta ko tunatarwa akan wani hadith ko wata surah haka.

 Application ne mai kyawun gaske sannan da sauki wajen amfani da shi. 

Sannan koda kana so ka saurari karatun wani malami idan ka kunna datar ka sannan ka saurari wata surah zaka iya kashe datar domin amfani da shi babu data.

 Ga link din Application din din a kasa sai ka taba ka sauke shi a wayar ka ta android.


Download

Previous Post Next Post