Kira kyuta a kowace kalar waya ( Fake call ) 2024

Kira kyuta a kowace kalar waya ( Fake call ) 2024



Assalamu alaikum barkan mu da warhaka. Yan'uwa yau darasin mu akan wani application ne da zai baka damar kiran waya kyuta batare da ko sisin ka ba amman na karya. Wato fake kenan. Wannan application din zai baka damar zabar suna da hoto da number waya sannan da lokachin da kake so ya kira ka shine zai dinga kiran ka adadin da ka zaba.

 Zakaga wani lokachin wani yakan iya bin wannan hanyar yayi amfani da ita yayi muku karya akan cewa babban wani mutum ko wanda aka sani ya kira shi. Kuma a gaban ku zakuga yana yin wayar domin har tafiyar mintuna app din zai nuna ma adadin da kake buqata. To amman wannan kiran wayar na karya ne domin babu wanda ya kira shi. Hasalima yayi amfani da makamanchin irin wannan application din ne.



 Baza ka taba ganewa wannan kiran na karya bane ko na gaskiya bane domin nasan zai iya nunama bama zaka iya jin muryar wanda ya kira ba. Sannan a wannan kiran zai iya saka hoton wanda yake so yayi karya dashi ko wanene a duniyar nan da kuma adadin yanda yake so ya dinga kiran sa da kuma lokachi da kwanan wata.

 To abinda yasa na kawo mana wannan application din bawai dan muyi karya dashi bane aa na kawo shine domin kaima kasan da irin application din domin dukkanin wanda akayi masa karya akan kiran da kuma sauraron kiran zaka iya cewa kasan yanda hanyar take.

 Wato application din zai matuqar baka mamakin da baka taba gani ba domin farko shi application din babu wahala wajen amfani da shi. bugu da qari zaka iya saitawa daidai lokachin da application din zai kiraka sannan da kuma adadin kiran da zai ma.



Misali kanason 2/3/2024 karfe 2:00pm to wannan kiran bazai shigo wayar ka ba sai wannan lokachin yayi. Sannan zakaga kiran ya shigo wayar ka da kuma adadin da kake so wannan kiran yayta maimaituwa. Misali ba sau daya ba sannan ba sau biyu ba. Adadin da kake so.

Ga link din application din a kasa sai ka taba kaima ka mallake shi sannan ka gwada da kanka. Kaga yanda aikin nashi yake.

Zakaga an rubuta download da koren rubutu sai ka taba shine zai baka damar saukewa akan wayar ka.




Download

Previous Post Next Post