Yanda zaka hana a kira ka da private number a wayar ka koda bakayi save din number ba

Yanda zaka hana a kira ka da private number a wayar ka koda bakayi save din number ba



Assalamu alaikum barkan mu da warhaka ina fatan kuna cikin koshin lafiya. 

Yan'uwa yau darasin mu akan application din zai baka damar control din duk wani kiran waya da akeyima a waya.

 Abubuwan da wannan application din yake kunshe dasu shine.

 Da farko zaka iya zabar number mutum daya kayi blocking din number wayar sa. Sannan babu yanda zai iya kiran ka.

 Abu na biyu zaka iya kulle dukkanin hanyar da idan bakayi save din ta a wayar ka ba kiran bazai shigo ba. Saboda wani lokachin zakaga ana yawan kiran wayar ka sannan bakayi save din number wayar sa ba. Inde kayi amfani da wannan application din zaka iya hana duk wata number da baka save din number wayar sa ba.

 Abu na uku akwai wanda zakaga aba yawan kiran su da private number. koda kayi blocking din number wayar mutum zai iya kulle number sa ya kira ka sannan kira ya shiga cikin wayar ka. To idan kayi amfani da wannan application din zaka iya saita duk wata number da aka boye a matsayin private zaka hana ta shiga cikin wayar taka.

Download

Previous Post Next Post