Yanda zaka kulle talla ta daina fitowa acikin waya ko Application 2024

 Yanda zaka kulle talla ta daina fitowa acikin waya ko Application 2024


Assalamu alaikum barkan mu da warhaka yan'uwa yau darasin mu akan wani application ne da zai baka damar kulle duk tallolin da suke fitowa acikin wayar ko acikin app. 

Da dama zakaga idan kana amfani da wani application to acikin sa akwai tallan da take fitowa wani lokachin ma har jikin screen din wayar ka take fitowa gaba daya duk ta dame ka.

 To idan ka mallaki wannan application zaka iya kulle dyk tallolin da suke acikin ko wane kalar application sannan kayi amfani da shi batare da tallan ba.

 Da zarar kana so ka kulle tallan sai ka shiga cikin application zakaga wajen kunnawa a tsakiya. Da zarar ka danna ta sai ka fita daga app din shine app din ya kunna a duk bangarorin wayar ka zai kulle ma tallolin da suke damun ka.


Kamar yanda kuke ganin hoton sama a tsakiy zakuga wata babbar makumna wadda itace zaka dinga kunna wa sannan idan kana so normal yayi sai ka kashe.

 Sannan applivation din zai fada ma adadin dukkanin tallan da take fitowa a duk wani application a wayar ka. Koda kuwa wannan application din a background din wayar ka yake.

 Akwai wasu application da su suna amfani da background koda baka shiga cikin su ba. Amman suna daukar bayanai sannan idan akwai talloli sukan nuna acikin app din. Shine ma wani lokachin zakaga tallan tana fitowa ajikin screen din wayar taka..



Ga link din Application din a kasa zakaga an rubuta download sai ka taba ka dauke shi acikin wayar ka.

 BAYANI.: Amman apolication din sai ka biya kudi. Da free ne amman yanzu sai ka biya kudi sannan zakayi amfani da shi. Niyu iya dubawa ta bansamo muku mai saukin amfani ba sai na kudi. Hakan yasa insha Allah banda wannan  application din akwai link da ake sakawa a cikin setting din waya. Zanyi muku wannan videon insha Allah.

 Amman shi wannan application din dukkanin masu amfani da wayar android ko iphone zasu iya amfani da wannan application din. Amman shi link din kawai iya android ne zasuyi amfani dashi. Dukda shi na link din zanyi muku videon sa nan gaba.


Download

Previous Post Next Post