Zakayi chatting da kowane kalar yare a kowace kalar waya 2024

Zakayi chatting da kowane kalar yare a kowace kalar waya 2024


Assalamu alaikum barkan mu da warhaka yan'uwa ma'abota wannan shafi mai albarka. Yau darasin mu akan wani application ne da zai baka kayi chatting da kowane kalar yare a wayar ka ta amfani da keyboard din wayar ka.



 Normal kamar kowane kalar keyboard yake sai de shi banbanchin sa da kowane keyboard shine zai baka dukkanin amsar tambayar da kake so yayi kayi masa. 



 Da farko de misali idan kana chat a kowane platform ko social media normal duk wanda ya turo ma da sakon turanchi kowani yare to shi keyboard din zai fassara ma zuwa yaren da kake buqata. Sannan haka idan kana so ka tura masa a yaren sa misali turanchi ne ko arabic ko france ko dukkanin yare. Da zarar ka rubuta da abinda kake so ko abinda ka iya shi wannan applicatiok din zai juyama shi zuwa yaren da kake so na turanchin ko arabic din da dai sauran su.



 Sannan koda kuna magana da mutum sai kake so ka tura masa magana amman baka san yanda zaka rubuta ba to shi wannan application din da zarar ka bashi topic da kanshi zai rubuta ma dukkanin abinda ya kunshi abinda kake so ka rubuta din. 

Misali kana so kace ya baka kudin da kake binshi bashi da zarar ka rubuta ( Give me money ). To akwai inda zaka danna a keyboard din wanda zai juyama sannan ya rubuta ma duk abinda ya kunshi wannan give me money din. 



 Sannan shi keybaod din zaka iya magana da shi bangaren tambayar shi fassarar wata kalma ko yanayin lokachi ko location da dai sauran su.

 Akwai application din na kowane wayoyi iphone ko android amman na ajje muku link din android din  gashi nan a kasa sai ka taba ka sauke shi a wayar ka.


Download

Previous Post Next Post