Sabon Application da zai nuna ma hanyar unguwa ko gari

 

Sabon Application da zai nuna ma hanyar unguwa ko gari 



Assalamu alaikum barkan mu da warhaka yan'uwa yau darasin mu akan wani application ne da zai baka damar gano ko tantance dukkanim wata hanyar da kake so kaje wani gari ko unguwa ko wani guri na daban.

 Tuntuni google suna da irin wannan Application din sai de kuma da yawa basa amfani da shi. Hakan yasa na kawo mana wani sabon application din da zai baka damar gano hanya koda baka san da ita ba.

 Kawai abinda zaka yi shine da zarar ka shiga cikin application din sannan ka rubuta sunan garin ko unguwar ko gurin misali office ko wani masallachi. To shi wannan application din zai dinga nunama hanyar da ta dace har zuwa inda ka rubuta masa. Bigu da qari zai dinga fadama inda zakayi idan kana so kuma ka kunna.



 Misali idan kazo wajen kwana to application din zai dinga fadama gurin. Sannan zaka iya adding din gidan ka ko office naka kanayin amfani dashi. Koda misali bako ne kai a garin da kaje ko unguwar kuma kana so ka fita zuwa wani guri to sai ka shiga cikin application din kayi adding din unguwar yanda idan ka tashi dawowa normal application din zai kwatanta maks har inda kazo din.

 Sannan koda ace ka shiga garin ko state din sannan kana buqatar samun wani hotel ko restaurant ko wani guri da zakayi amfani dashi. To ba sai kayi tambaya ba shi application din akwai inda zsks taba kana tabawa zai nuno ma duk abubuwn da zaka iya buqata. To sai ka zabi restaurant din ko hotels din ko wani gurin da kake so kaje.

 Idan ka taba zakaga duk abubuwan da suka shafi wannan hotels din kudin su da kuma yaushe suke budewa harda number wayar su. idan kana so

ka tambaye su kenan.


Kana tabawa zakaga direction idan ka taba shine application din zai kaika har gurin batare da kayi tambaya ba.

 Ga link din application din a kasa zakaga an rubuta download sai ka taba ka sauke shi akan wayar ka.


Download

Previous Post Next Post