Yanda zaka kama wanda ya Taba ma waya ko ya sace 2024

 Yanda zaka kama wanda ya Taba ma waya ko ya sace 2024



Assalamu alaikum barkan mu da warha yan'uwa ya ibadah ya kuma qara hakuri da mu. Bisa rashin yawan amsa tambayoyin da kuke yi mana.

 Allah ya karbi ibadun mu baki daya. Darasin mu yau shine zai baka damar gane dukkanin wanda ya daukar ma waya idan ka ajje ko kuma idan an sace ma ita gaba daya. Zakaga hoton sa.

 Wannan Application yana da matuqar amfani kwarai da gaske wajen gane wanda yake daukar ma waya yayi ma bincike acikin sa.


Yanda application din yake amfani shine. Da zarar ka dakko application din ka saka shi acikin wayar ka zai baka damar saka gmail din ka normal wanda shi ne zai dinga ajje ma hotunan da shi application din yake dauka a ciki.

 Abu na farko idan kana so kagane wanda yake daukar ma wayar shine idan ka dauki wayar taja kuma ka saka password a jikin wayar to dukkanin wanda yayi kokarin cire wannan password din wayar taka. shi application din zai dauki hoton wanda yake daukar waya sannan ya ajje ma shi acikin application din.

Da zarar ka bude application din dukkanin hotunan zaka gansu ta ciki.

Kaga zaka gane dukkanin wanda yake daukar wayar taka bayan ka ajje a gida ko ka saka chaji.

 Sannan idan sace ta akayi zaka iya ganin hotunan ta cikin gmail din da ka saka. Zakaga hoton sa gaba daya.

Ga link din application din a kasa zakaga na rubuta download a koren rubutu sai ka taba ka sauke shi a wayar ka.


Download

Previous Post Next Post