Yanda zakayi control din wayar ka batare da ka taba ta ba😍 2024

 





Yanda zakayi control din wayar ka batare da ka taba ta ba😍 2024



Assalamu alaikum barkan mu da warhaka yan'uwa kwana biyu tun cikin azumi bamu samu munyi wani post ba.

Amman insha Allah yanzu mundawo da zafin mu. Jinkirin da aka dan samu ma wasu dan matsalolinne wanda insha Allah komai yazo karshe. Ku cigaba da yi mana addua. Mungode.

Yau darasin mu akan wani application ne da zai baka damar control din wayar ka batare da ka taba ta ba. Wannan application din dukkanin wani abu da ya danganchi notification din wayar ka ita wayar taka da kanta zata karanta ma shi ya danganta da yanda ka saita application din.



Abubuwan da wannan application din ya kunsa suna da yawa sosai amman zan danyi mana karin bayani kadan daga ciki.

Akwai abinda ya danganchi kiran waya da kuma message da kuma time na dukkanin lokutan da kake so ya fitar ma da notifications.

 Shi amfanin application din idan ka saita shi shine zai dinga fadama dukkanin wani notification da ya shigo cikin wayar ka.

 Misali dukkanin sakon nin da aka turo ma wato ( Messages ). abind aya danganchi whatsapp da dukkanin sakonnin da aka turo ma. to koda wayar tana nesa da kai ka ajje ta idan an turo ma ita wayar da kanta zata fada ma sunan wanda ya turo ma da dukkanin sakonnin da ya turoma.

Haka zai dinga fadama dukkanin numbobin da aka kira ka. Da kuma wand aya kira ka.

Haka zalika zai fadama abinda ya danganchi time wato lokachi.

  Shi dai wannan application din zai taimaka ma sosai wajen ganin batare da ka taba wayar ka ba koda kana aiki wayar kuma tana nesa dukkanin abin notification zai dinga fadama.

 Ga link din application din a kasa zakaga an rubuta download sai ka taba ka sauke shi acikin wayar ka.

👇👇👇👇👇👇👇👇

Download

Previous Post Next Post