Best Image resizer|| Na Kowace kalar waya 2024

 Best Image resizer|| Na Kowace kalar waya 2024



Assalamu alaikum barkan mu da warhaka ya gari ya kuma zafi. Allah ya qara mana lafiya da kafiyar gari baki daya ameen.

 Yan'uwa yau akan wani application ne darasin namu wanda zai baka damar gyara dukkanin hoton ka duk wani abu da kake da buqata akan hoton. Misali. Rage nauyin hoto rage Girman hoto qara quality hoto.

 Wannan abinda na lissafa a sama kadan daga cikin abubuwan da suke cikin application din ne.

  Da farko da yawa zaka sami hoto a wayar ka amman a iya hoto daya zaka iya samun sa yana da girman MB kusan 100mb a iya hoto daya musamman a dauki hoto a wayar iphone. To zakaga duk ya shanye maka storage din wayar ka baka sani ba gaba daya. Sannan shi nauyin hoton yakan sa idan kana so kayi amfani da hoton a wani guri ko wani application din zasu fada ma iya dadin MB da suke so hoton ya kasance. Idan kayi amfani da wannan application din zaka iya rage hoto duk nauyin sa sannan ka zabi adadin MB da kake so shi hoton ya koma. Sannan zaka iya zabar adadin hotunan duk yawan su kayi musu editing ko resize din a lokachi daya.



 Bayan nan zaka iya saita girman hoto zuwa yanda kake so. Nasan akwai wadanda saboda rashin amfani da social media ko website hakan zasuyi mamaki. Amman zan baku misali yanda zaku gane akan rage girman hoton. Wani lokachin idan kana so kayi amfani da hoto ka dora akan dp din whatsapp to zakaga wannan hoton baya fitowa full inde ba iphone kake amfani da ita ba. Koda ma iphone din ce zakaga idan kayi kokarin duka full din hoton ya fito zakaga baya clear sosai.

To Koda ma de wace kalar waya kake amfani da ita wannan Application din zai baka damar rage girman hoton ka dora shi a DP na whatsapp din ka. Banda DP ma akwai ART na Youtube akwai na Facebook wanda babu yanda normal full hoton ya fito duka idan zaka dora a akan abinda kake so kayi amfani da ita.



Akwai de abubuwa da yawa wanda kake so kayi amfani da shi aciki sai ka mallaki application din sannan zaka gano yanda zakayi amfani da shi.

 Ga link din Application din a kasa zakaga an rubuta download a karshen rubutun sannan da koren rubutu sai ka taba ka sauke shi a wayar ka domin fara amfani dashi.



👇👇👇👇👇

Download

Previous Post Next Post