Assalamu alaikum barkan mu da sake kasancewa a sabon darasin namu.
Yau darasin mu akan wani application ne da zai baka damar hana dukkanin wanda yake son ya dinga amfani da wayar ka koda ka chanja password din wayar ka.
Shi wannan Application amfanin sa shine zai baka damar bude password din wayar ka ta amfani da agogon wayar ka.
Sau dadama kakansamu kanka wani lokachin idan ka ajje wayar ka a gida a wani waje haka amman za'a samu wani yana daukar ma waya kamar matar ka ko yaran ka. Ko abokanan ka. To koda ace ka chanja password din wayar dole wata rana sai sun gano saboda zaka iya budewa a wajen su ko a gaban su.
To amfanin wannan Application din shine dukkanin yanda ka saita password din ta amfani da agogon waya ko ta date and time ne. Misali idan ta agogon wayar ka ka saita to dukkanin wannan lokachin da yayi da mintunan da yayi a wannan lokachin dashi zaka dinga amfani kana bude wannan wayar taka. Misali. Yanzu ace karfe 8:29. To idan ka tashi bude wannan oassword din na wayar taka zakayi amfani da wannan code din na wannan time din. 8:29 sai ka saka shi akan 829 to shine zai bude wannan wayar taka. Sannan koda bayan ka bude wannan wayar again kana so ka qara bude idan agogon ya qara harbawa akan karfe 8:30 to zaka saka password akan 830 shine zai bude. Dukkanin de wani time da lokachin d ayake a wannan lokachin zai dinga bude ma password din wayar taka.
Sannanidan da date and time kayi amfani shina zaka dinga saitawa a wanan ranar misali. Yau 5/05/2024 to zaka dinga bude wannan agogon wayar ka a 5052024 gaba a ranar idan kuma an qara kwana to kaga an koma 6/05/2024 zakayi amfani da 6052024 normal de tanda ranar take. Dukda de zan baku shawarar kuyi amfani da time saboda shine duk kowane lokachi zai dinga chanjawa. To kaga koda wani yaga wannan password din to a banza saboda duk bayan adadin lokachi ko minti yake chanjawa.
Ga link din application din a kasa
Zakaga an rubutu download da koren rubutu sai ka taba shine zaka sauke applicatiokm din