Yanda zaka dauki videon sirri DA zaka hana daukar Hoto a wayar ka 2024





 Assalamu alaikum barkan mu da warhaka ya zafi Allah de ya shiga lamarin mu ameen ya hayyu ya qayyum.

Yan'uwa wasu application guda biyu na kawo mana wanda suna da matuqar amfani sosai. Kowannan su amfanin sa daban hakan yasa na zabo mana su domin fara amfani dasu acikin wayoyin su. 

 Application ne na farko zai baka damar daukar videon sirri na video zai baka damar kashe ko hana camerar wayar ka tayi amfani koda anyi kokarin amfani da ita.

 KARIN BAYANI



 (1) Application na farko zai baka damar daukar videon sirri koda an hana yin video a gurin sannan koda baka so a gane kana daukar video a gurin sannan a wayar ka batare da ka dakko wayar taka ka dannan camera ka kuma rike wayar a hannun ka ba.

 Da farko zaka iya saitawa lokachin da ita wayar taka da kanta zata fara daukar video a gurin misali. Idan zaka je gurin kamar karfe 5:00pm to tun kana gida zaka iya saita application din domin ya daukar ma video. Zaka iya saita 5:30pm wato a kaje gurin da mintuna 30 kenan shine zayyi record na video da zarar lokachin yayi.



 Batare da ka dakko wayar taka ka danna ko ka rike a hannu ba karka kuma damu idan wayar a security take ko kuma an kira ka a waya dukkanin wadannan abubuwan bazasu hana wayar daukar video a lokachin ba. Kawai abinda zakayi shine ka saita wayar yanda camerar normal zata fito misali a riketa a hannu kamar kana chattin ko kamar ka daga waya ko a ajje wayar a gaban aljihu wanda zata dauki videon mai kyu sosai.

 Sannan kowace camera wayar zatayi aiki wajen saitawa idan camera gaba ko ta baya duka zaka saita. Kai akwai abubuwa da yawa wanda ita wannan camera ko videon bazasu baka matsala wajen daukar videon ma.

 Link din sa yana kasa zakaga an rubuta download 1 da koren rubutu sai ka taba shine zaka sauke applocation din a wayar ka.


 (2) Application ma biyu zai baka damar saita camerar wayar ka taqiyin aiki. Misali koda an dauki wayar ka za'ayi hoto da ita to inde ka shiga applocation din ka kunna shi a lokachin camerar bazatayi aiki  ba. Ana shiga camerar zata nuna tana da matsala. To zaka sami sauki wajen abokai ko kanne wanda suke yawan arar wayar ka koda kana amfani da ita wajen daukar hoto.



 Wani lokachin ma koda kayi kokarin sakawa wayar taka security zasu saka dole sai ka bude ka basu wayar. Amman idan kayi amfani da wannan application din to normal zakayi amfani dashi wajen kulle camerar wayar taka.

Ga link din shima a kasa zakaga an rubuta Download 2 da koren rubutu sai ka taba ka sauke shi a wayar ka domin amfani da shi. 



Dukkanin wadannan application suna da amfani sosai wajen ganin ka sarrafa wayar ka. Sannan koda ba yanzu zakayi amfani da application din ba to ka ajje yana da amfani sosai nan gaba.

Download 1

Download 2

Previous Post Next Post