Phone copy.
Assalmu alaikum barkan mu da warhaka ina muku fatan alkhair. Yau darasin mu akan application din da zai baka damar mayar ko tura dukkanin abubuwan da kake dashi a tsohuwar wayar ka zuwa sabuwar wayar da ka chanja.
Idan zaka chanja waya zakayi amfani da wannan application din wanda zai baka damar tura dukkanin abubuwan da suke a tsohon wayar ka kamar su. SMS,Contacts, Images,video,Calllog tare da decument harda calender.
Komai da komai kamar kayi copy din tsohuwar wayar taka zuwa sabuwa. Batare da ka rasa komai a wayar taka ba.
Masu amfani da iphone akwai hanyar da campanyn Apple din suka fito dashi wanda zaka iya transfer daga iphone din ka zuwa sabuwar da ka chanja.
Komai da komai harfa missedcalled din da akayi ma.
Sannan akwai wayoyi kala daban-daban kamar irin su huwei ko oneplus ko vivo to zakaga sai de wani application wanda aka ware daga asalin campanyn wayar wanda idan ka chanja waya zaka iya tura komai zuwa irin wayar.
Amman shi wannan application din kowace kalar waya zaka iya turawa daga tsohuwar wayar ka zuwa sabuwar batare da ka chanja ko ka rasa wani abu na cikin tsohuwar wayar taka ba.
Sannan koda chanja waya kayi misali daga iphone zuwa android ne wannan application din zai taimaka ma sosai. Domin wannan application din koda android din gare ka zaka iya amfani da wannan application ka tura komai daga androod zuwa iphone ko daga iphone zuwa android da dukkanin wasu kaloli na waya.
Ga link din Application din nan a kasa zakaga an rubuta download da koren rubutu sai ka taba ka sauke shi a wayar ka.