Daga yau an daina ganin sirrin ka na whatsapp inde ka mallaki wannan Application din 2024

Daga yau an daina ganin sirrin ka na whatsapp inde ka mallaki wannan Application din 2024





Assalamu alaikum barkan mu da sake kasancewa a yau a wani sabon videon. Yan'uwa yau darasin mu akan wani application ne da zai baka damar yin chat a whatsapp ko a kowane kafa ta social media babu wanda zai gane chat din koda yana bibiyar duk whatsapp chat da kakeyi.

 Wato abinda bamu sani ba shine da yawa dukkanin wasu abubuwa da mukeyi a whatsapp to akan iya bibiya sannan aga abinda muke tattaunawa kome nene amman bamu sani ba.

 Hakan yasa na kawo mana daya daga cikin abinda zaka kulle a daina ganin duk whatsapo message din da ka tura.

 Application ne da zai baka damar yin chat da wani yare wanda idan ka turawa wanda kuke chat din sai ka fada masa hanyar da zai bi a fassara wannan message din daka tura masa.

 Misali: Bayan ka tura masa sakon zaka iya kiran sa a waya ka fada masa hanyar sannan ka fada masa wannan sakon akwai password akan sa sai ka fada masa numbobin sirrin sannan zai gano yanda zai bude chat din.

 Duk da nasan har yanzu baku gane full abinda nake nufi ba.

 Da farko de shi wannan application din zai baka damar bayan ka dakko shi zaka shiga wajen inda zakayi dukkanin rubutun ka adadin yawan sakon da kake so ka rubuta.





Bayan ka rubuta kamar yanda misalin sa yake a cikin hoton sama zakaga save bayan ka dannan save wani gurin zai qara fito ma kamar yanda misalin yake acikin hoton kasa.






Download


 Shine zai nuno ma encrypt da kuma decrypt. To anan Farko tunda kai ne zaka juya wannan rubutun sannan ka boye shi sai ka dannan Encrypt din bayan ka danna shine zai chanja ma wannan yaren da ka rubutu zuwa wani yare daban. Bayan ka danna shine kuma zai qara baka damar ka saka password wanda zaka kulle wannan sakon da zaka tura dokin koda mutumin da yake bibiyar ka ya gano hanyar da zai bi yayi gane sirri to zaiga akwai password wanda shi bai san dashi ba.

 Bayan ka saita password shine zaka dannan continue kamar yanda yake a hoton sama.
Bayan nan shine zai baka damar copy na link na wannan abinda ka chanja gaba dayan sa sai ka turawa wanda zakuyi chat din  ta whatsapp ko ta wani chatting ko message haka.
 zakaga ya nuno ma kamar yanda misalin hoton kasa yake.

 To bayan ka tura masa sai ka fada masa ya dakko wannan application din sai yayi duk kamar yanda kaima kayi wajen rubutun.
 Sai de waje daya ne banbanchi. Kai farko ka danna Encrypt ne to shi Decrypt zai danna sannan ya saka password shine rubutun asali wanda ka chanja zai bude normal.
Ga misalin shi nan a kasa na hoton.

 To idan kabi ire-iren wadannan hanyoyi babu mai iya bibiyar ka koda ya sakama tsaro sosai a chat ko a wayar ka.
 Saboda haka na ajje link din application din a kasa zakaga an dubutu download da koren rubutu sai ka taba ka sauke shi a kan wayar ka 👉  Download



Previous Post Next Post