(Free Chat)Yanda zakayi chat ta bluetooth batare da DATA ko Internet ba 2024
Assalamu alaikum ina muku fatan alkhairi yan'uwa yau darasin mu akan wani application ne da zaia baka damar chat da wayar ka batare da kana da DATA ko internet ma a wayar taka ba. Ina maso korafin Datar wayar su tana qarewa da wuri sannan basa samun network din da sukeyin chat musamman da abokanan su ko kawayen su ko babban jiko masoyan su. Wannan applocation duk zai magance muku ire-iren wadannan matsalar. Wato shine wannan chat da na kawo muku saukin sa yayi yawa bugu da qari ma babu yanda zaka nayin chat ka sami matsalar tura sako ko video ko hoto saboda babu ma network din gaba daya. Zan yi muku bayanin yanda asalin application din yake da kuma abubuwan da ya kunsa.
Application din ya kunshi abubuwa da yawa kamar irin.
(1) Zakayi chat da duk wanda kake so inde ya bude bluetooth din wayar sa
(2) Babu matsalar data ko internet gaba daya
(3) Kamar yanda kake chat a sauran social media
(4) Zaka tura hoto
(5) zaka tura video
(6) zakayi voice duk a cikin wannan chat din.
(7)Zaka iya kiran wanda kuke chat din dashi kuyi waya ta cikin app din kuma free ne
Ga misalan abubuwan da ya kunsa a hoton kasa.
Babban makasudun amfani da wannan application din shine.
Babu ta yanda zaka ga abinda ka tura na chat din ya sami delay wajen shi. Saboda kwata-kwata ba internet a tafiyar sa ballantana lokachin tura shi a sami matsalar internet har ka tura yaqi zuwa.
Inde ka kunna bluetooth din wayar ka sannan ka shiga cikin application din to duk wanda yake online zaka ganshi.
Idan assli ka tashi bude application din baya buqatar number wayar ko gmail ko wani abu wanda zaka bude account din dashi.
Koda kaje garin da babu internet gaba daya zaka iya amfani dashi musamman ma family ko abokai.
Da zarar dukkanin ku kun hau online acikin application zaku more wannan chatting babu matsalar data.
Dukkanin mai budurwa musamman wanda take kusa da gida ko kusa da unguwa zaka iya amfani da wannan application na free kira da kuma free chat.
Ga dai link din Application din a kasa zakaga an rubuta download da koren rubutu sai ka taba ka sauke shi a wayar ka.