Ka Gaggauta mallakar wannan Application din kafin ka chanja waya 2024

 


Daga yau an daina cutar ka idan kaje chanja waya 2024




Assalamu alaikum barkan mu da sake kasancewa a wani sabon videon. Yan'uwa yau wannan application yana da amfanin da ya kamata ka mallake shi kafin ka chanja waya musamman a wannan yanayi na cutar da akeyi mana lokachin da muka je siyan waya ko chanja waya.

 Abinda ya ke faruwa shine dukkanin wasu kasuwannin wayoyi inda ake siyar da waya inde ka sayi waya ba sabuwa ba to zasu baka wani Adadi na kwanaki domin gano wata matsala akan wayar wanda idan kaga wannan matsalar zaka iya mayar musu dashi. Idan kuma baka samu ba har wannan adadin lokachin ya wuce to koda kaga wata matsala baza ka dawo musu da wayar su chanja ma ba. Wani lokachin ma zakaniya siyan waya wajen abokin ka ko wanda ka sani amman a sami irin wannan matsala kaga anzo anayin fada ko ba'a rabu lafiya ba.

 Hakan yasa na kawo mana wannan application din da zai baka damar  binciko dukkanin wasu matsaloli da kuma lafiyar wayar kafin ma ka tafi daga wajen da ka sayi wayar ba.

 Idan ka mallaki wannan application din kawai abin da zakayi shine  idan ka sayi wayar sai ka saka application din a wayar bayan nan sai ka bude application din ta nan ne zaka ga fanni daban-daban na test din dukkanin wasu abubuwa ma wayar abinda ya danganchi network ko camera ko sound ko

bettery da dai sauran dukkanin abinda ya danganchi wayar. Koda ma wayar tana daukar zafi shi wannan application din zai baka damar ganowa. Idan har kaga babu wata matsalar a wayar to zaka iya siyan ta. Idan kuma kaga tana da matsala to normal zaka iya mayar da wayar domin tana da matsala.







Ga link din application din a kasa zakaga  an rubuta download da koren rubutu sai ka tana ka sauke a wayar ka.




Downlod

Previous Post Next Post