Wannan Application din zai Rubuta duk maganar da kayi acikin video abin mamaki 2024 ( Caption Text ).

 Wannan Application din zai Rubuta duk maganar da kayi acikin video abin mamaki 2024 ( Caption Text ).



Assalamu alaikum barkan mu da dake kasanwace a wani sabon videon. Yan'uwa yau darasin mu akan wani application da zai taimaka ma wajen gano duk wani abu da ka fada sannan ya rubuta ma shi a kasan videon ka wanda koda kana da mabiya basa gane yaren ka to zai fassara ma zuwa yaren ka kake so.

 Akwai masu videos kala daban-daban wanda zakaga iya hausa ne kawai sukeyi acikin videon amman kuma akwai wadanda basa iya gane mai yake fada sai de suna bibiyar sa  a kowane video ko darasi da yayi. To shi wannan application din zai baka dama rubuta dukkanin abinda ka fada a cikin videon nanka.



 Akwai hanya kala daban wanda shi wannan application din zai fassara ma. Misali idan kayi videon zaka iya amfani da AUTO Generate wanda shi wannan application din zai fassara duka abin da ka fada aciki amman shi wannan Hanyar bazatayi da hausa ba sai de videon da ka yi shi da turanchi saboda a cikin application babu hausa.

 Akwai hanyar da zaka iya rubuta dukkanin wata kalma da ka fada da kanka sannan ka jerata inda kake so domin videon naka yayo tsari mai kyu. Wannan shine zai taimaka ma koda ba da turan chi kayi videon ba zaka iya rubuta dukkanin abinda kake so ma'ana dukkanin yaren da kake so koda kuwa hausar ne ko turanchin ne.

Akwai hanya ta uku wadda idan kana buqatar shi applocation din ya rubuta duk abinda zai iya jan hankali akan videon naka zaka iya amfani da Ai na application din sannan ka fada masa Title na videon naka shi kuma da kansa zai dunga rubuta abinda zai iya jan hankalai akai. Itama wannan Hanya dole sai de da wani yare na daban ba Hausa ba. Saboda babu hausa acikin yarikan da suke cikin Application din.



Maganar design na Text din wajen launi mai kyu akwai su kala-kala sannan zaka iya amfani da shi kanshi Application din wajen editing din videon naka yayi kyu sosai.



Ga link din Application din a kasa zakaga an rubua download sai ka taba ka sauke shi acikin wayar ka.

Download

Previous Post Next Post