Yanda zaka gano camerar da take daukar bayanan ka 2024
Assalamu alaikum barkan mu da warhaka ya zafi ya kuma rayuwa Allah ya shige mana gaba ameen.
Yan'uwa yau darasin mu akan wani application ne wanda zai taimaka ma dukkanin wani sirri da za'a iya fitar dashi baka sani ba bangaren daukar videon sirri naka. Misali wannan application din zai gano ma dukkanin wata camera da aka boye ana daukar bayanan ka a hotels ko a office ko kuma zaka hadu da wani mutumin wanda zakuyi wata maganar sirri dashi akan iya sakama wata camera wadda zata dauki wani sirri wanda baka bata tunanin camera bace. Wata camerar zakaganta kamar Biro wata kuma kamar zobe ko maballi ya kan iya daukar wani video na sirri wanda kawai dan ya tozarta ka amman bazaka taba ganewa ba. Idan kuma a hotel ne akan iya ajjewa inda baza ka taba ganewa ba ko a office din ka ko cikin mota. Idan ka mallaki wannan application din zai nunama dukkanin wata camera da take daukar irin wannan videon sirri.
Kamar yanda kuke gani a cikin hoton sama zakaga yanda camerar wayar ka zata nunama asalin wasu alamu wanda anan camersr aka ajje ma.
Ba iya wannan ba shi wannan application din zai baka damar gano duk wata wifi ko wani application wanda shima yakan iya daukar sirrin ka baka sani ba. Akwai wanda wani wifi din zakaganshi free ne amman kuma yana daukar bayanai har yayi ma hacking na wani abu naka musamman a hotels ko a wani babba guri haka. To wannan Application din zai gano wannan wifi din idan yana da matsala da duk wani application ma.
Ya kamata ka mallaki wannan application din saboda yana da amfani sosai domin zaman lafiyar ka musamman manyan mutane.
Ga link din Application din nan a kasa zakaga an rubuta download da koren rubutu sai ka taba ka sauke app din a wayar ka.