Yanda zaka gane wanda yake bibiyar duk chat da kiran wayar ka baka sani ba 2024
Assalamu alaikum barkan mu da sake kasancewa a sabon darasin namu. Yan'uwa yau darasin mu akan wani application da zai baka damar gano dukkanin wata kafa da ake bibiyar wayar ka baka sani ba. Wato a rayuwar nan akwai abubuwan da yaka mata mu kula dasu musamman bangaren waya mutum baka damu dashi ba amman kai ya damu da kai. Misali asalin wanda ka sayi wayar a hannun sa ko asalin wayar da ka siya akwai wani application da aka saka ma kuma ya bibiyi kiran wayar ka ko camerar wayar ka ko dukkanin hotuna ko video hadi da location din asalin inda kake. Da yawa zakaga akan iya yi maka wani hacking amman ka rasa wane hanya aka bi akayi maka wannan hacking din.
To abinda yake faruwa wani lokachin akan iya biniyar wayar ka ta wani application din da zai dauki data din wayar ka gaba daya. Dukkanin wani password da username da sauran abubuwan da na lissafo a baya. ko asalin wanda ka sani yakan iya saka ma wani application din sannan a boye maka a cikin wayar ka wanda gaba daya bazaka gane ba. Domin yana amfani da background din wayar ka. Sannan ya dauki bayanan ka baka sani ba.
To amfanin wannan application din zai baka damar gano wasu application din da suke bibiyar ka. Sannan zai fito ma application din ya kuma baka damar cire application din a wayar ka.
Wannan shine a takaice bayanin application din.
Ga link din Application din a kasa zakaga an rubuta download da koren rubutu sai ka taba ka sauke application din a wayar ka