Yanda zaka hada Cartoon video ka Sami kudi
Assalamu alaikum barkan mu da warhaka yan'uwa na a muslunchi. Yau darasin mu akan wani application ne wanda kuka dade kuna jiran ku mallake shi. Duk da nasan daman kuna jira wata rana zakuga nayi muku video akan sa sannan na baku link din sa.
Dukkanin wani application da kake buqata kawai ka jira kuma ka bibiye mu koda bakayi tambaya ba to ina tabbatar ma insha Allah wata rana zakaga nayi video akan sa.
Wannan application din zai baka damar hada video na hoto ya koma yana magana kamar yanda zamugani yana yawo a social media ire-iren videos din.
Akwai website da application da yawa wanda yake ba da damar hada AI na hoto wani ma kawai fada masa zakayi ko ka rubuta masa zai zana ma duk abinda ka rubuta masa. Hatta bangaren video haka yake zaka iya rubuta masa ya hada ma video. To amman shi ire-iren wannan applocation wanda na kawo mana ya banbanta da ire-iren su.
Domin shi wannan zaka yi voice ko waka ko wani audio sannan ka saka Avatar ko AI ko ka saka hoton ka ko hoton wani sannan yayi videon muryar da kake buqata ko ka saka.
Nayi bayani sosai a videon da na dora a tiktok da facebook dina duk da abin gaba daya bashi da wata wahala wajen hadawa.
Kana bude application din zakaga create idan ka taba kawai zakaga wajen Voice da script da kuma Avatar to wadannan guraren koda baka gane komai a ciki ba normal kana tabawa zakaga sunyi ma bayanin da kuma misalai na yanda kake so komai naka ya kasance.
Ga link din Application din a kasa zakaga an rubuta download da koren rubutu sai ka taba ka sauke shi a wayar ka sannan ka fara amfani da shi.