Yanda zaka hada wayar ka da Computer ta amfani sa File manager 2024

 Yanda zaka hada wayar ka da Computer ta amfani sa File manager 2024






Assalamu alaikum barkan mu da warhaka yan'uwa. Ina fatan kowa yana cikin koshin lafiya. Allah yasa hakan ameen.

Yan'uwa yau darasin mu akan wani application ne mai matuqar amfani sosai akan waya da kuma computer. Domin zai baka damar amfani da file manager sannan zaka iya hada waya da computer ya amfani da wannan application din batare da kayi amfani da USB ba.


(1) Abu na farko shi wannan application din zakayi amfani da shine a matsayin file manager wanda zaka dinga bude komai da yake akan wayar ka ko memory ta cikin sa. Sannan zakga adadin abubuwan da suke acikin wayar taka. Da folders da duk abinda ya danganchi yana yi na Storage na kan wayar da kuma memory idan akwai shi akan wayar kenan.

Sannan zakaga adadin abinda yafi yawa a wayar taka.


(1) Na biyu zaka iya hada wayar ka da computer normal batare da kayi amfani da USB cable ba. Kawai kana amfani da IP na kan wayar ko application din to normal zaka iya tura abinda kake so daga kan wayar ka zuwa computer ko daga computer zuwa wayar taka.


 Sannan zaka iya amfani da dukkanin illahirin wayar taka ta cikin computer din. Akwai yanda zak iya amfani da QRCode ta cikin application din wajen scan.

(3) Dukkanin wasu folders ko wani file idan ya hade ko ya boye ita wannan file manager zata baka damae fitoma da ita waje sannan idan kana so kayi deleted din sa zak iya amfani da application din.



 (4) Abu na hudu ko nace na karshe zaka yi amfani da abubuwa da yawa abinda ya danganchi mutiple window. Wato koda ka bude application din zaka iya amfani da screen biyu. Koda kana amfani da shi application din sannan zaka iya amfani da multiple kayi kallo ko kayi chat duk a screen na wayar.

 Idan ka danna zaka rana screen din rabi a sama rabi a kasa.

Akwai qrcode da kuma dukkanin illahirin Apps na wayar ka da saura abubuwa na bangaren hada computer da kuma wayar.


Ga link din Application din sai ka taba ka sauke zakaga an rubutu download da koren rubutu👉👉Download

Previous Post Next Post