Yanda zaka kulle duk wata Talla da take fitowa a wayar ka 2024

 Yanda zaka kulle duk wata Talla da take fitowa a wayar ka 2024



Assalamu alaikum barkan mu da wannan lokachin yan'uwa ya fama da wannan yanayin da muke ciki. Allah ya fiddamu ya saka albarka a rayuwar mu ameen.

 Yan'uwa kamar kullum de yau darasin mu akan wani application ne wanda zai baka damar hana talla ta daina fitar mana akan wayar ka. Akwai masu amfani da dukkanin wayoyin musamman android wani lokachin zakaga talla tana takura ma musamman a cikin wasu applications idan zakayi amfani dashi. Dole wadannan application din inde kana amfani dasu sai de ka biya kudi sannan zakayi amfani da application din wanda babu talla acikin  sa.

 Hakan yasa na waro mana wannan application da zakayi amfani da shi wajen kulle dukkanin tallolin da su ke fitowa afikin application. 

 Bugu da qari zaka iya amfani da VPN wanda zaka iya chanja location kayi amfani da network din wata kasa daban.


Shi VPN din na cikin wannan application din zaka iya chanja dukkanin kasar da kake so. Kamar yanda kuke ganin misali a hoton sa.

Da farko idan ka dakko application din ka bude shi. Idan zaka bude sauran application din sai ka shiga cikin application din zakaga wajen kunnawa da zarar ka dannan wannan wajen shine zaka kulle duk talla gaba daya da take amfani da shi a wayar ka. Ga misalin cikin application din a hoton kasa.


Wannan makunnane da kuke gani a tsakiya ita zaka danna kama damna ta shine dukkanin tallolin da suke a wayar ka na app zasu kulle gaba daya.

 Sannan idan zaka kashe application din sai ka qara danna kan application din.


Shine duk wani abinda ya danganchi VPN din zaiyi amfani dashi a wayar ka da kuma kulle tallolin na wayar ka.


Sannan zai lissafa duk tafiyar kulle tallolin na dukkanin sassan wayar ka.

Kamar yanda kuke gani misalin sa a hoton sama.

 Ga link din application din a kasa zakaga an rubuta download da koren rubutu sai ka taba ka sauke shi a wayar ka.


Download

Previous Post Next Post