Yanda zakayi amfani da kowane Banki wajen cire kudi ta cikin wannan Application din 2024

 

Yanda zakayi amfani da kowane Banki wajen cire kudi ta cikin wannan Application din 2024





Assalamu alaikum barkan mu da warhaka barkan mu da rana ko da wannan lokachi. Ya jimamin abinda yake faruwa a yau ko nace a kwana biyun nan na Chanja sarki da gwamnan kano abba kabir yusuf  ( Abba gida-gida ).yayi ranar Alhamis. Allah yasa hakan shi yafi alkahiri ameen.

 Yan'uwa yau darasin mu akan kudi ne😀 Wato akan banki ne domin dukkanin abinda ya shafi banki ai kamar ya shafi kudi ne.

Domin wannan application din zai baka damar gano ko amfani da dukkanin wani secret code na kowane banki sannan kayi amfani da shi koda baka da babbar waya ko baka da network a wayar ka.

 Sau tari mukan amfani da banki amman bamusan yanda zamuyi amfani da USSD code wajen amfani da bankin mu cikin sauki ba.

Saboda kana so kayi transfer ko ka sayi katin waya amman baka da DATA a wayar ka ko gaba daya baka da babbar waya ma. To amman zakaga bakasan Code da zakayi amfani da bankin wajen tura kudi ko siyan DATA ko siyan Kati ta bankin ka sannan ta Code ba.

 Hakan yasa na kawo mana wannan application din domin zaka sami dukkanin wani code wanda sakayi amfani dashi. 

Sannan kaima zaka taimakawa wani dan'uwan naka ko wanda ka sani domin dukkanin wani code na kowane banki normal zakayi amfani da shi. Batare da kana da babbar waya ba.




 Kowane banki da yake a nan nigeria akwai code din da zakayi amfani da shi kamar yanda kake amfani da application na banki sannan ba sai kaje POS ka duba balance ko transfer ba.

 Saboda haka ne na zabo mana wannan application abin mamaki wanda zai baka damar amfani da kowane banki.

 Ga link din application din zakaga an rubuta download da koren rubutu sai ka taba ka sauke shi akan wayar ka domin fara amfani da shi.👉👉👉👉Download

Previous Post Next Post