Yanda zakayi chat a whatsapo ko baka da DATA a wayar ka 2024

 

Yanda zakayi chat a whatsapo ko baka da DATA a wayar ka 2024



Assalamu alaikum barkan mu da warhaka yan'uwa.  a Gurguje yau darasin mu akan wani application ne da zai baka damar chat a whatsapp ko babu DATA a wayar ka koda kuma baka online a wannan lokachin. Saboda application ne da zai baka damar tura sako lokachi da rana da dukkanin abinda kake so wanann sakon ya kunsa. Hoto ko video ko voice ko sticker sannan wanann sakon ya shiga koda baka online a wannan lokachin. Sannan adadin mutanen da kake buqata wannan sakon yajewa.



 Idan ka tashi ka mallaki wannan application din normal Zaka bude shi sannan ka zabi abinda kake so kayi na tura sakon sa kuma zabar irin whatsapp din da kake amfani dashi kamar whatsapp normal ko whatsapo business da sauran su. To bayan ka bude shi zai baka damar rubuta wanan sakon. Misali kamar bikin ka ya kusa kuma kana tsoron kada wannan lokachin yayi sannan kayi mistake wajen rashin tunawa da wani wajen tura masa sanarwar daurin auren naka ko muka wata sanarwa ta daban.




 Zaka rubuta wannan messages din da kuma duk wani hoto ko voice ko wani audio haka. Idan ka zaba zai baka damar maeking din duk adadin mutanen da kake so ka turawa wannan sakon. Da kuma Rana da kwanan wata da lokachi gaba daya. Bayan ka saita wannan messages din sai kayi save din sa. Bayan kayi save to koda baka online koda kuma ka manta da wannan message din inde lokachin yayi shi wannan application zai tura wannan sakon zuwa wadanda ka zaba a wayar taka ko a whatsapp din naka.




 Bugu da qari zaka iya saita auto reply wajen shi whatsapp din naka yana tura sako na wani adadin kalmimi da ka saita.

 Aarain bayani akan Auti reply. Zaka iya zabar dukkanin wanda ya turo ma magana acikin maganar akwai (Aure). To zaka iya saita wata magana wanda kake so shi wannan application din ya tura masa da sakon. Ko ka saita duk wanda yace ma Goodmorning to iya shi kadai wannan sakon zai jewa.




 Wannan shine kadan daga cikin takaitaccen misalai da zan baya akan wannan appication.

 Saboda haka ga link din sa nan a kasa zakaga an rubuta download da koren rubutu sai ka taba ka sauke shi a wayar ka.



Download

Previous Post Next Post