Yanda zakayi Control din wayar ka Batare da ka TABA ta ba ( Blind ) 2024

 Yanda zakayi Control din wayar ka Batare da ka TABA ta ba ( Blind ) 2024


Assalamu alaikum barkan mu da sake kasancewa a yau a sabon darasin namu.

Yau darasin mu akan wasu application guda biyu ne wanda zasu baka damar control din wayar ka batare da ka taba ta ba. Musamman Wadanda Allah ya jarabta da rashin gani.


Application na farko zai baka damar fadawa wayar ka dukkanin wani abu da kake so tayi ma. Abinda ya danganchi kiran waya ko ta kunna video ko wani sauti na Audio. Kawai fada mata zakayi ita da kanta zata fadama ko tayi abinda kace tayi.

 Zaka iya tambayar ta lokachi ko ka tambaye ta yanayin gari ko wani abinda ka kake buqata. Kaga normak idan ka sakawa wanda baya gani Application din zai taimake shi.

 Link din sa yana kasa zakaga an rubuta download (1) da koren rubutu amman sai ka bi a hankali wajen gane rubutun.






Application na Biyu zai baka damar wayar ka ta dinga fadama dukkanin wani kiran waya ko text message da akayima a wayar ka. Zata fadama wanda yake kiran wayar taka tare da fadar sunan sa. Sannan bangaren messages zai fadama wanda ya turo sakon da kuma abinda aka turo ma koda wayar bata kuda dakai. Harda bangaren whatsapp idan wayar taka aka turoma messages ta whatsapp wayar taka zata fadama sunan wanda ya turoma tare da fadar dukkanin wani sakonna da ya turoma.

 To kaga idan mutum baya gani bayan an saita masa a wayar sa kawai wayar zata dinga fada masa dukkanin sakonnin da kuma wanda ya turo da sakonnin.


 Link din sa yana kasa zakaga an rubuta download (2) da koren rubutu amman sai ka bi a hankali wajen gane rubutun.





Application na uku ko nace na karshe zai baka damar karanta ma dukkanin wani text na rubutu a website ko a wani social media ko wani rubutu. Kawai kanayin Mark din dukkanin rubutun Application din zai karanta ma.

Link din sa yana kasa zakaga an rubuta download (3) da koren rubutu amman sai ka bi a hankali wajen gane rubutun.





 To dukkanin wadannan application guda uku suna da amfani sosai musamman wadanda Allah ya jaranta da rashin gani.




Download (1)

Download (2)

Download (3)

Previous Post Next Post