Wayar ka tana daukar zafi?. Da Shan chaji? Wannan Application shine mafita

 

Wayar ka tana daukar zafi?. Da Shan chaji? Wannan Application shine mafita




Assalamu alaikum barkan mu da warhaka. Yan'uwa yau darasin mu akan wani application ne da zai ba wayar ka kariya busa zafin da take dauka da kuma shan chaji na battery da takeyi. Musamman a wannan yanayi na zafi mukan riski wannan mataki akan wayoyin mu.

 Wani lokachin haka kawai sai kaga wayar ka tana daukar zafi ko bakayi amfani da ita ba kawai sai kaga chajin yana qarewa da wuri.

  To acikin dalilan da suke daka wannan wayar a wannan mataki shine acikin application din wayar ka akwai wanda suke amfani da background din wayar ka wanda koda baka shiga cikin application din ba su kan yi aikin da suka saba sannan koda ka kunna data baka shiga ba zasuyi amfani da wannandatar har kaga sun shanye ma DATA.



 To da taimakon wannan application din zaka iya gano dukkanin wani application wanda yake amfani da backgroun din wayar ka sannan ka kashe shi wanda shine zai bawa wayar ka lafiya sosai.

 Link din application din yana kasa ka duba. Amman kafin na ajje link din zan danyi muku qarin bayani akan kula da wayar ka wajen shan chaji da kuma daukar zafin da takeyi.

 Abu na farko de ka mallaki wannan application din sannan ka saka acikin wayar ka.

 Na biyu ka sami chaji wadda take daidai da wayar ka wadda batafi karfin battery na wayar ka ba ko bata wuce ba. Saboda wani looachin kana saka mata chaji karama wadda bata chaja wannan wayar normal ko ka saka chaja wadda tafi karfin battery wayar. To wadannan ma suna taimakawa wajen rage karfin battery da kuma daukar zafin da takeyi.

 Na uku ka dinga kashewa wayar ka koda ba kullum ba a sati sau uku ko sau biyu a kashe ta danyi rabin awa ko awa daya a kashe domin itama ta dinga hutawa. Saboda muna amfani da wayoyin mu gaba daya ba ruwan mu da kashe su domin su huta.

 Sannan idan kaji wayar taka zafin jikin ta yayi yawa ka dinga samun abin sanyi kana dora mata. Kamar ruwa pure water kenan koda kuwa ba iphone bace ai itama tana son sanyi ko androdi din ce kuwa.

Mu kula wajenamfani da ita musamman a wannan yanayi na zafi. 

 To inde ka dan bi wannan hanyoyi wayar ka lafiya zakayi rayuwa da ita battery da ta baka matsala ko ta dauke gaba daya ba.

 Ga link din Application din sai ka taba ka sauke shi a wayar ka👉👉Download

Previous Post Next Post