Yanda zaka gano mai kiran ka da private number sannan kayi kulle ( Block ) din sa 2024

Yanda zaka gano mai kiran ka da  private  number sannan kayi kulle ( Block ) din sa 2024


Assalamu alaikum barkan mu da wannan lokachi. Yan'uwa yau darasin mu akan wani application ne da zai baka damar rufe dukkanin wata number waya da aka saka ta a private number babu yanda za'a iya kiran ka da ita ko da wayar ka a bude take.



Da farko de wannan application din amfanin sa ba iya nan ya tsaya ba. Zaka iya kulle dukkanin wata number waya wadda bakayi save din sunan ta a wayar ka ba. Inde ka kunna wannan acikin application din babu wanda zai kira number wayar ka ta shiga har sai de idan kayi save din number sa wato sai ka sanshi kenan. Akwai wani lokachin zakaga gaba daya kayi kokarin kiran wani babban mutumin amman kaga number bata tafiya kuma ace ma itace yake amfani da ita amman kai gaba daya bata shiga ko sau daya.

 To akwai hanyoyin da sukan bi su kulle dukkanin wani kiran waya da zai zo cikin wayar tasu to inde basuyi save din number ba kiran bazai shga ba.



 Idan ka mallaki wannan application din zai taimaka ma sosai wajen wannan da kuma kulle dukkanin wata number waya da aka sata a private number.

 Da dai wasu abubuwa da yawa wanda zaka iya saitawa a wayar taka.

 Ka mallaki application din shine zakaga cikakken dukkanin abubuwan da application din ya kunsa.

 Sannan nayi bayanin sa cikakke acikin youtube channel dina.


Ga link din Application din sai ka taba ka sauke shi a wayar ka👉👉Download

Previous Post Next Post