Yanda zaka hada katin daurin aure a wayar ka ka sami kudi kuma yayi kyu kamar a Computer 2024

 Yanda zaka hada Invitation a wayar ka ka sami kudi kuma yayi kyu kamar a Computer 2024



Assalamu alaikum barkan mu da warhaka yan'uwa yau darasin mu akan wasu application ne da zasu baka damar hada invitation kowane kala harda na Daurin aure ka sami kudi batare da kayi amfani da computer kuma ka sha wahala ba.

 Application ne guda biyu amman kowannen su akwai aikin su sannan dukkanin wanda ka zaba zaka iya hadawa batare da ka mallaki duka biyun ba.

 Sai de banbanchin su anan shine na farko shi zai baka damar hada invitation wanda baya motsi wanda ake turawa a waya sanann zaka iya print din sa ka rabawa mutane a takarda sannan babu wanda zai ce a waya aka hada shi saboda kyu sa.

 Shi kuma application na biyu zai baka damar hada invitation mai dan motsi kadan wanda a cikin sakonni zai dinga motsi suna da suna haka. Sannan iya a waya ake amfani dashi.

Amman dukkanin su na zabo sune wanda zaka iya hadawa batare da idan ka hada anyi tunanin a waya aka hada ba. Saboda yanda yazo da abubuwa masu kyu.

 Application na farkon wanda zaka hada katin daurin aure a wayar ka sannan zaka iya print din sa. 

Ga misalin ire-iren abubuwan sa na template din da yake cikin application din.

👇👇👇👇👇👇





Ga link din sa sai ka taba ka sauke shi a wayar ka👉👉👉Download


Application na biyu  wanda zaka hada katin daurin aure mai motsi ga link din sa sai ka taba ka sauke shina wayar ka domin fara amfani da shi👉👉👉Download

Sannan ga misalan hotunan sa nan a kasa.

👇👇👇👇👇👇






Previous Post Next Post