Yanda zaka Katse duk hanyar da za'a saurarin kiran wayar ka 2024

Yanda zaka Katse duk hanyar da zaka saurarin kiran wayar ka 2024



Assalamu alaikum barkan mu da warhaka yan'uwa ina muku fatan alkhairi. Da fatan muna cikin koshin lafiya Allah yasa Haka. Allah ya kawo mana sauki cikin Al'amuran mu Ameen.

 Yan'uwa kamar kullum yau darasin da zan koya mana akan wani application mai mahimmanchin gaske ne wanda zai baka tsaro akan dukkanin kiran number wayar ka. 

Sau Dadama mukan sami matsala idan mun ajje waya a gida akan iya kiran wayar mu sannan a sami akasi matan mu su dauka ko yaran mu ko kuma wani lokachin idan ka ajje abokin ka ya daga wannan kiran wayar.

To wani lokachin zakaga baka buqatar idan an kirawo ka wani ya daga misali kamar matar ka ta kira ka wani abokin ka ko wani daban ya daga wayar ko kuma a kira ka idan wayar tana cikin gida a sami matsalar matar ka ta daga ko kuma yayan ka.

 To hakan yasa na kawo mana wannan application din da zai baka damar kulle daidaikun wasu numbobi wanda inde aka kira ka to baza a iya daga wannan kiran wayar ba sai an saka passoword.

Misali zaka iya zabar number matar ka inde ta kira ka a wayar to sai an saka password sannan wannan kiran za'a iya daga shi. Ko kuma wata number daban. Sannan zaka iya zabar numba daya ko duk adadin da kake so wanda zaka iya kulle wannan kiran wayar.

 KARIN BAYANI

Karin bayani akan wannan application din.

(1) Zaka saka password ne ta cikin application din wanda zai kulle ma dukkanin wasu numbobi idan suka kira ka batare da yayi amfani da security na wayar ka ba. Koda ace matar ka tasan security na wayar ka to zaka iya zabar wani securityn daban wanda zaka sakawa wannan number wayar.





(2) Sannan wannan securityn sai irin wanda ka zaba misali akwai na Zane wato (Pattern) Akwai Pin wanda zaka saka Numbobi sannan akwai password wanda zaka iya rubuta wani kalma ko wani abin daban.




(3) Zaka iya zaban kalar yanda kake so shi wannan kiran wyaar ya kasance wanda ko da matar taka tana amfani da wayar ko abokin naka inde kana nesa k hango irin yanda screen din ya kasance to kasan babu wanda ya isa ya dauki wannan wayar. Kada ma kaje dan kaji wayar tayi ring ka rikice har wani ya zargi kamar wannan kiran wayar bakaso a dauke shi.

Akwai abubuwa da yawa wanda wannan Application din yazo dashi wanda ya kamata ace kayi amfani dashi acikin wayar ka.

Sannan banbanchin wannan application din da kuma videon da nayi abu biyu ne. Na farko shi wannan Application din zakaniya zabar number da duk kiran da tayi ma zatazo da security akai sai an bude wannan securityn sannan za'a iya daga wayar. Na biyu shi videon da nayi nace zaka iya amfani da lokachi wanda zaka kulle duk wani kiran waya da zai shigo cikin wayar ka ta amfani da security.


Ga link din Application din sai ka taba ka sauke shi.👉👉Download





Previous Post Next Post