JBT. Yanda zakayi register na TIN Number cikin sauki 2024

 



JBT. Yanda zakayi register na TIN Number cikin sauki 2024



Assalamu alaikum barkan mu da warhaka yan'uwa. Yau darasin mu akan wani application ne da zai baka damar kirkirar TIN number wadda da yawa muna shan wahala wajen bude wannan Tin number.

 Sannan akwai account na wani website ko application da zasu buqachi wannan Tin din to wani lokachin zakaga sai kaje ka biya kudi sannan za'a bude ma.

 Shi yasa na binciko mana wani application din da zai taimaka ma wajen bude wannan TIN number din batare da ka sha wahala ba.

 TIN Number shima de kamar NIN da BVN yake sai de kowane akwai inda suke amfani.

Shi NIN bangaren National ID card ne shi kuma BVN bangaren duk wani abu na banki. To shi TIN bangaren biyan Haraji ne domin zaka iya wayar gari kamar misali yanzu da facebook suka fara biyan duk dan Nigeria kudi to zakaga sai sun buqachi wannan TIN din. Sannan inde kana harkad online ko aikin gomnati wata rana zaka tsinchi kanka akan ka sami wannan TIN number take.

Saboda haka ga link din application zakaga an rubuta download da koren rubutu sai ka taba ka sauke shi a wayar ka domin fara amfani da shi.👉👉Download

Previous Post Next Post