Abin MAMAKI Yanda zakayi Control na wayar ka batare da ka Taba ba 2024

 


Assalamu alaikum warahmatullah. Barkan mu da warhaka yan'uwa ya sanyi ina muku fatan alkhairi.

A Gurguje yau darasin mu akan wani application ne da yake da amfani saboda zai baka damar control ko amfani da wayar ka batare da ka taba ta ba.

Abinda ya danganchi kiran waya ko turo sako ko bangaren whatsapp gaba daya.

 Idan ka saita application din a wayar ka zai dinga fada ma dukkanin wanda ya turo ma da wannan sakon da kuma karanta sakon koda wayar bata kusa da kai batare ma da ka cire wayar daka chaji ko security ba. Haka bangaren kiran waya shima nan zaka iya saitawa ta dinga fada ma dukkanin wanda ya kira ka a waya sunan sa koda ma baka rubuta sunan ba zata iya fada ma dukkanin numbobin da aka kira ka da su.



Bugu da qari zaka iya daka flash wato fitils kenan. Zaka dinga yin haske bangaren camerar ka. Bangaren kiran waya da kuma bangaren turo sakon.

 Kamar yanda nayi muku takaitattun bayani akan wannan application na tabbatar da cewa zaka gano yana da amfani.



Saboda idan babu wannan application din inde aka kira ka a waya dole sai ka dakko wayar sannan ka duba wanda ya kira ka.  Haka bangaren sakon wato SMS da kuma whatsapp. Zakaga abin yana ta baka wahala wajen amfani da wannan bangaren.

To shi application din zai saukaka ma dukkanin abinda na lissafo.

Ga link din application din a kasa zakaga an rubuta download da koren rubutu sai ka taba ka sauke shi a wayar ka.

👇👇😀

Download

Previous Post Next Post