Yanda zaka dauki record din sirri ba'a sani ba 2024
Assalamu alaikum . Yan'uwa yau darasin mu akan application din da zai baka damar daukar record din sirri batare da an sani ba.
Domin zaka iya saita lokachin da kake buqata wayar tayi ma record batare da ka danna record din ballantana ka cire ta daga security.
Sa farko shi dai wannan application din wajen daukar sauti yana dauki mai qualityn gaske koda wayar bata da MIC sosai.
Sannan kamar yanda nayi muku bayanin a farko na saita lokachi da kuma rana wanda kake so wayar taka ta fara record.
To sannan akwai hanyar da zaka iya saitawa da zarar ka Girgiza wayar taka to zata fara record. Misali shima yana da amfani sosai domin koda bakasan da lokachin da zaka fara record din ba. To a wajen ba tare da ka dakko wayar ka cire ta daga secirity sannan ka bude app din ka danna record ba. Kawai kana girgiza ta wayar zata fara record kamar de yanda ka saba. Sannan da quality mai kyu.
Bayannan zaka iya amfani da wannan application din bangaren daukar karatu kamar wani malami yana huduba ko karatu a masallachi ko kuma a makaranta anayin lecture.
To ba damar ka ajje wayar ka sannan idan malamin zai fara wa'azin ace ka dakko wayar taka sannan ka danna record duba da yanda masallachin yake bama lalle a barka kaje inda malamin yake ba.
To zaka iya amfani da wannan application ka saita lokachi da rana da mintuna gaba daya kawai sai ka ajje wayar taka koda malamin ya fara karatun lokcahin da ka saita acikin application din yana yi wayar zata fara record na wannan karatun.
Ga link din application din a kasa zakaga na rubuta download da koren rubutu sai ka taba ka sauke shi a wayar ka.
👇👇👇👇👇