Yanda zaka kama wanda ya daukar ma waya
Assalamu alaikum barkan mu da warhaka yan'uwa ina muku fatan alkhairi. Ya sanyi ya gari ya kuma al'amura ina muku fatan alkhairi.
Yan'uwa har kullum mun kawo muku darasi masu amfani. Yau ma wani application na kawo mana wanda zai baka damar gano duk lokachin da aka taba ma waya bayan ka ajje ko wayar tana aljihu zatayi kara sosai.
Zaka gane wannan lokachin ana kokarin daukar wayar taka ne.
Wato shi wannan application din idan ka saita shi koda a gida ne ka ajje wayar ka ko ka saka a chaji to idan aka zo daukar wanann wayar zatayi qara matuqar gaske har sai ka gane an dauki wannan wayar. Sannan koda acikin mutane ne wayar kuma tana aljihu aka yi kokarin taba wayar ko dauka ita ma nan zatayi qara sosai har sai ka gane an taba ta.
Kamar de yanda nayi muku bayani a cikin videon to haka application din yake. Bayan nan application din bashi da nauyi sannan bashi da wahalar saitawa domin yanda suka saukaka amfani da shi.
Yana da mabiya da yawan wajen amfani da shi da kuma inganchin sa.
Ga link din application a kasa an rubuta download kana tabawa shine application din zai sauka akan wayar ka sai kayi amfani dashi.
👇👇👇👇